Da wane dalili masu tuƙa Keke Napep suka shiga yajin aiki a Damaturu?

0
154

Daga Ibraheem El-Tafseer

A wani yunƙuri na magance cin zarafi da tarar da ta wuce ƙima da hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Yobe (YROTA) ke ci gaba da yi, direbobin babur masu ƙafa uku da aka fi sani da Keke Napep sun fara yajin aikin a ranar Talata 13 ga watan Fabrairu. Ma’aikatan YOROTA suna cin zarafi mai yawa ga masu tuƙa Keke NAPEP, waɗanda kuma suke karɓar tara mai yawa kan ƙananan laifukan da suka shafi ababen hawa.

Mambobin ƙungiyar Keke Napep da suka zanta da manema labarai a Damaturu, sun bayyana takaicinsu kan lamarin. Sun bayyana rashin adalcin da suke fuskanta da kuma tara ta kuɗi mai da ‘yan YOROTA take ɗora masu. A sakamakon wannan yajin aikin, matafiya da suka haɗa da ɗalibai, ma’aikatan gwamnati, ‘yan makaranta, da sauran jama’a, abin ya shafa, inda aka tilasta musu yin tafiya mai nisa a ƙafa don isa wuraren da za su je. Wannan musamman ya shafi waɗanda ke fama a cikin mawuyacin yanayi na tattalin arziƙi na yanzu.

Bugu da ƙari, yajin aikin ya yi illa ga harkokin kasuwanci da makarantu, musamman ga waɗanda ke nesa da gidajen ma’aikatansu ko ɗaliban. Jama’a na ƙira ga gwamnatin jihar da ta shiga tsakani tare da samar da wasu matakai na gaggawa domin rage wahalhalun da matafiya da ‘yan kasuwa ke fuskanta.

Tattalin arziƙin jihar Yobe da ma ƙasa baki ɗaya ya ƙara taɓarɓarewa sakamakon ƙarancin kuɗi da ƙarancin hanyoyin rayuwa. Yana da matuƙar muhimmanci Gwamnatin Jiha ta magance wannan lamarin cikin gaggawa, duba da irin ƙalubalen tattalin arziƙi da al’umma ke fuskanta.

KU KUMA KARANTA: Masu tuƙa Keke Napep a Yobe, sun koka akan takurawar da hukumar YOROTA ke yi musu

Ta hanyar ɗaukar matakin gaggawa don magance matsalolin da masu aikin Keke Napep suka nuna, gwamnati za ta iya taimakawa wajen dawo da tsarin sufuri da kuma rage wahalhalun da jama’a ke fuskanta.

A halin da ake ciki, ƙoƙarin tuntuɓar hukumar ta YOROTA domin jin ra’ayinsu bai yi nasara ba, domin har zuwa lokacin rubuta wannan rahoto ba a amsa ƙiran wayar wakilinmu ba. Wannan ya nuna gaggawar lamarin da kuma buƙatar ɗaukar matakin gaggawa don dawo da tsarin sufuri da kuma rage wahalhalun da jama’a ke fuskanta.

Leave a Reply