No menu items!

Sample Page Title

Date:

Da ni ake haɗa baki, ake garkuwa da mutane a jihar Katsina – Hakimin Runka (Bidiyo)

Hakimin Runka ta jihar Katsina, Injiniya Salisu Abdul’aziz Runka ya faɗa da bakinsa, cewa shi ne yake baiwa ‘yan bandits, (masu garkuwa da mutane) bayanai, na yadda za su sace mutane a jihar Katsina. Runka ya bayyana haka ne a wani faifayin bidiyo da jami’an tsaron ‘Community Protection Guards’ na jihar Katsina suka kama shi.

A cikin bidiyon yace, ba tursasa shi aka yi ba, ya ce tun da asirinsa ya tonu, gara kawai ya fallasa komai. Ya fara ne da bayyana waɗanda suke harkar ‘Informants’ ɗin tare, irin su Alhaji Ruga Kachalla, ɗan cikin garin Runka ne. Amma yanzu haka yana cikin daji. Sai Sani Mohoɗinge da Usman Manu Gurgu. Da waɗannan mutane nake harka. Inji shi.

Ya ce “Na shafe shekaru 4 ina hulɗa da su, wato ina kai musu bayanai na yadda za su su yi garkuwa da mutane. Ina da masaniya da kuma hanuna dumu-dumu a shigowar masu garkuwa da mutane cikin garin Runka.

Shigowarsu ta farko, sun ƙira ni ta waya, akan za su shigo Runka su ɗauki mutane. Alhaji Kachalla Ruga ne ya ƙira ni. Da suka zo Runka ni na ba su mutane 12 a gidan Alhaji Mu’azu Runka. Sai na ba su mutane 5 a gidan Salmanu. Dukkansu ‘yan fada ne, a fada suke.

KU KUMA KARANTA: Yadda uba ya haɗa baki da ɗansa ya yi wa ;yarsa ciki

A dukkan waɗannan mutane an karɓi kuɗin fansa Naira miliyan 25, da babura 2. A cikin kuɗin, ni da Garba Ware-Ware (Sarkin Baƙi) an ba mu Naira dubu ɗari takwas. Kowa a cikinmu zai ɗauki Naira dubu ɗari huɗu (400,000). Shi ma a nan Runka yake. Shi aka bawa kuɗin ma ya kawo min nawa. Amma shi ban san adadin mutanen da ya ba su ba.

Ina nadamar wannan abu da na yi, yanzu haka ma a cikin nadama nake.

Kalli bidiyon a nan:

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...