Da gangan yaran da aka kama a zanga-zanga suka faɗi a kotu – Sufeton ‘Yansandan Najeriya
Daga Ibraheem El-Tafseer
Sufeto-Janar na ‘yansanda, Kayode Egbetokun, ya bayyana cewa yanke jiki da faɗuwa da wasu yara shida da ake zargi da zanga-zangar #EndBadGovernment suka yi a kotu kafin gabatar da su a gaban Alƙali ya kasance wani shiri ne da aka tsara don jan hankalin jama’a ga abin da ba daidai ba.
Egbetokun ya jaddada cewa, duk da haka, an ba da taimakon likita cikin gaggawa, ya na mai bayyana cewa ‘yansanda su na da alhakin kula da lafiyar waɗanda suke tsare.
A ranar Juma’a, an gurfanar da mutane 76, yawancinsu ƙananan yara waɗanda ke fama da rashin isasshen abinci, a gaban kotu dangane da zanga-zangar #EndBadGovernance. Goma sha shida daga cikinsu sun faɗi kuma aka fitar da su daga cikin kotun.
Bayan gurfanar da su, kotu ta ba kowanne yaro beli wanda aka sa a kan Naira miliyan goma. Wannan al’amari ya haifar da suka a gida da waje.
KU KUMA KARANTA: Dokar ;yancin yara ba ta yarda a gabatar da yara a kotu ba, ballantana hukuncin kisa ; Babban Lauya
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa a wata sanarwa mai kwanan wata Nuwamba 1, da mai magana da yawun rundunar Muyiwa Adejobi ya sanya wa hannu a madadin Sufeto-Janar din, Egbetokun ya tabbatar da cewa, a karkashin dokar Najeriya, wadanda suka kai shekarun aikata laifuka sun isa a hukunta su duk da karancin shekarunsu.
Ya ce, “A yau, wani abu da ba a zata ba ya faru a kotu inda wasu shida daga cikin wadanda ake zargi suka yi gaggawar fita daga kotu kuma suka yanke jiki suka fadi , suna jan hankalin kafofin watsa labarai a wani yunkuri da aka shirya don jan hankali ga abin da ba daidai ba.”
“A kwanan nan rundunar ƴansanda ta ƙasa ta gurfanar da mutane 76 da ake zargi da aikata ta’addanci, cin amanar kasa da kone-kone. Wadannan Laifuka ne manya da su ka sa ake tsare da wadanda ake zargi.
“Tun lokacin da aka fara shari’ar nan, rundunar ƴansanda ta dage wajen bin ƙa’idojin Shari’a domin yi wa waɗanda ake zargin adalci,” in ji shi.