Da ƙyar na sha a Yemen – Shugaban WHO

0
11
Da ƙyar na sha a Yemen - Shugaban WHO

Da ƙyar na sha a Yemen – Shugaban WHO

Darakta-Janar na hukumar ta WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce bama-baman da suka fada kan ginin suna da matukar ta da hankali, ta yadda kunnuwansa suka yi ta rugugi har ‘yan kwanaki bayan harin.

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ya ce ba shi da tabbacin cewa zai iya tsira da rayuwarsa a wani harin da jiragen saman yakin Isra’ila ta kai kan babban filin jirgin saman Yemen, a cikin jerin hare-haren da take kaiwa kan ‘yan tawayen Houthi masu alaka da Iran.

Darakta-Janar na hukumar ta WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce bama-baman da suka fada kan ginin suna da matukar ta da hankali, ta yadda kunnuwansa suka yi ta rugugi har ‘yan kwanaki bayan harin.

Tedros ya ce nan take aka tabbatar cewa an kai harin ne a filin jirgin, yana mai bayyana yadda mutane suka shiga rudani a wurin, bayan fashewar wasu bama-bamai kusan hudu, daya daga cikinsu kusa da inda yake zaune dab da dakin jiran matafiya.

“Ban tabbata a zahiri cewa zan iya tsira ba saboda ya yi kusa da ni sosai, ‘yan mitoci kadan daga inda muke,” kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Tedros ya ce shi da takwarorinsa sun makale a filin jirgin saman na tsawon sa’a guda ko abin da ya fi haka, a yayin da yayi ta jiyo karar abin da ya yi zaton jiragen sama marasa matuka ne ke shawagi a sama, lamarin da ya haddasa damuwar cewa za su iya sake bude wuta.

Harin na Isra’ila kan Yemen ya auku ne bayan da mayakan Houthi suka yi ta harba rokoki da makamai zuwa Isra’ila, a wani abin da suka bayyana a matsayin nuna goyon baya ga Falasdinawa a Gaza.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya fada daga bisani cewa, yanzu ne Isra’ila ta fara sa hannu kan fafatawa da ‘yan Houthi.

Kamfanin dillancin labarai na Saba da ke karkashin ikon Houthi ya ce mutane uku ne suka mutu a harin da aka kai a tashar jirgin saman, sannan an kashe wasu uku a Hodeidah, yayin da wasu 40 suka jikkata a hare-haren.

Leave a Reply