Cuɗeni-in-cuɗeka shi ne ginshiƙin hulɗar ƙasa da ƙasa – Farfesa Gambari

0
273
Cuɗeni-in-cuɗeka shi ne ginshiƙin hulɗar ƙasa da ƙasa – Farfesa Gambari
Farfesa Gambari na jawabi a taron

Cuɗeni-in-cuɗeka shi ne ginshiƙin hulɗar ƙasa da ƙasa – Farfesa Gambari

Daga Idris Umar, Zariya

Tsohon Ministan Harkokin Waje kuma Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, ya bayyana cewa cuɗani in cuɗaka (reciprocity) shi ne ginshikin huldar kasa da kasa. Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a matsayin Bakon Musamman a taron koli na farko da Kungiyar Tsofaffin Daliban Nazarin Harkokin Kasa ta Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya ta shirya.

An gudanar da taron ne a Cibiyar CBN ta Tattalin Arziki da Kudi da ke ABU Zariya, domin girmama tsoffin shugabannin tsohuwar Fakultin Fasaha da Kimiyyar Zamantakewa (FASS), tare da hadin gwiwar MacArthur Foundation. Taken taron shi ne: “Girman Ilimin Afirka: Tasirinsa ga Siyasa da Cigaban Afirka.”

Farfesa Gambari, wanda ya taba shugabantar Sashen Kimiyyar Siyasa a jami’ar ABU, kuma wanda ya kafa shirin Nazarin Huldar Kasa da Kasa a makarantar, ya ce gogewarsa a jami’ar ce ta taimaka masa sosai a aikin diflomasiyya. Ya yabawa jami’ar da sashen wajen horas da manyan jakadun Najeriya da suka taka rawar gani a duniya. Har ila yau, ya godewa masu shirya taron bisa yadda suka yaba da gudummawar tsoffin malamai.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin tarayya ta bawa kamfanin jirgin sama na Tanzania lasisin fara jigila kai tsaye zuwa Legas 

A jawabin bude taron, Farfesa Attahiru Jega, tsohon shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) kuma shugaban taron, ya jinjinawa kungiyar tsoffin dalibai bisa tunanin girmama manyan malaman da suka kafa tarihi a jami’ar. Ya bayyana FASS a matsayin “al’umma ce ta masana da malamai daga kowane fanni.” Haka kuma, ya godewa Farfesa Gambari bisa jagoranci da kokarinsa wajen bunkasa fannin nazarin kasa da kasa a Najeriya.

Da yake wakiltar Shugaban Jami’ar ABU, Farfesa Adamu Ahmed, Mataimakin Shugaban Jami’a mai kula da Cigaba da Bincike, Farfesa Sanusi Aliyu Rafindadi, ya bayyana cewa ABU ta bayar da gudummawa wajen samar da fitattun jakadu da diflomas a Najeriya. Ya kuma yabawa rawar da Farfesa Jega ya taka a lokacin da yake Shugaban Kungiyar ASUU wajen kare martabar malamai a kasar nan.

Shugaban Kungiyar Tsofaffin Daliban Nazarin Huldar Kasa da Kasa na kasa baki daya, Jakada Muntari Abdu Kaita, ya bayyana cewa shirya taron wata hanya ce ta nuna godiya ga makarantar da ta gina su. Ya kuma godewa Farfesa Gambari da Farfesa Jega bisa yadda suka amsa gayyatar su zuwa taron.

A jawabin da ya gabatar mai taken “Girman Ilimin Afirka: Tasirinsa ga Siyasa da Cigaban Afirka,” Farfesa David Moveh daga Sashen Kimiyyar Siyasa da Nazarin Huldar Kasa da Kasa, ya bayyana cewa FASS ta horar da dama daga cikin masu hangen nesa da masu tasiri a harkokin siyasa da cigaban kasa. Ya bayyana Malam Farfesa Abdullahi Smith a matsayin wanda ya assasa Makarantar Tarihin Zariya, wadda ta taka rawar gani wajen kawar da ra’ayin cewa Afirka ba ta da tarihi.

A sakon gaisuwa, Dr Kole Shettima, Daraktan MacArthur Foundation Afrika, ya yabawa shirin girmama manyan malaman da suka sadaukar da rayuwarsu don ci gaban dan Adam. Ya kuma bayyana cewa za a ci gaba da girmama marigayi Farfesa Abdullahi Mahadi da irin su.

Sarkin Zazzau, Mai Martaba Malam Ahmad Nuhu Bamalli, CFR, wanda Arc. Haruna Abubakar Bamalli, Barden Kerarriyan Zazzau, ya wakilta, ya bayyana farin cikinsa da kasancewa cikin jerin masu karramawa. Ya kuma bukaci kungiyar da ta ci gaba da irin wannan kokari don taimakon jami’ar.

A madadin wadanda aka karrama, Farfesa Uka Ezenwe ya bayyana godiya ga kungiyar tsoffin daliban bisa wannan girmamawa da aka yi musu, yana mai cewa hakan ya kara musu kwarin gwiwa kan sadaukarwar da suka yi wa ilimi da kasa.

A karshe, an mika lambobin yabo ga tsoffin shugabannin FASS da wasu fitattun mutane a wajen taron.

Leave a Reply