Cire tallafin mai a Najeriya na neman durƙusar da matatun man Turai

0
291

Daga Ibraheem El-Tafseer

Kawo ƙarshen biyan tallafin man da gwamnatin Najeriya ke zubawa domin sauƙaƙawa jama’ar ƙasar raɗaɗin tsadar sa na barazana ga makomar matatun ƙasashen Turai waɗanda ke samun maƙudan kuɗaɗen shigar da ake sayen tacaccen man ana kaiwa ƙasar.

Waɗannan matatu na Turai sun dogara ne da tace man suna aikewa da shi zuwa arewacin Amurka da Yammacin Afirka, cikin su harda Najeriya, ƙasar dake fitar da mai mai yawan da ba ta iya amfani da shi, amma rashin matatun da za’a tacesu a cikin gida ke haifar mata da matsala.

Raguwar man da kamfanonin ko matatun Turai ke samarwa na ci gaba da raguwa a ‘yan shekarun da suka gabata, sakamakon gasar dake fitowa daga Gabas ta Tsakiya da Amurka da kuma Asia waɗanda suke tace man da kan su.

KU KUMA KARANTA: Masu sayar da man fetur na arewa sun yi barazanar shiga yajin aiki

Rahotanni sun ce ribar da ake samu a arewa maso yammacin Turai ya tsaya akan Dala 27 kowacce ganga, yayin da alƙaluma ke nuna cewar buƙatar kan ƙaru a yankin Amurka ta Arewa sakamakon wasu matsalolin da suke hana samun man mai inganci.

Sai dai masana sun ce raguwar buƙatar man daga Najeriya zai ci gaba da yin illa ga matatun Turai saboda ganin yadda man da take buƙata ya ragu saboda daidaita farashin sa sakamakon cire tallafin.

Sabon shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cire tallafin mai ranar da aka rantsar da shi, abin da ke sanya gwamnati na asarar aƙalla Dala biliyan 10 kowace shekara, yayin da yawan man da ake amfani da shi a cikin gida ya ragu da kashi 28.

Alƙaluma sun ce hannayen jarin man a Najeriya ya tashi zuwa tan dubu 960 zuwa tan dubu 613 tsakanin watan janairu zuwa Yunin wannan shekara.

Bayanai sun ce safarar man da ake ta ɓarauniyar hanyar zuwa ƙasashen Togo da Jamhuriyar Benin da Kamaru da kuma Nijar ya ragu sosai saboda tashin farashin sa.

Leave a Reply