Cin hanci da rashawa wata gagarumar matsala ce da ke addabar gabashin Afirka – Beti Kamya
A cewar shugabar hukumar yaƙi da cin hanci ta Uganda, Beti Kamya Turwomwe, ƙasar na asarar sama da tiriliyan 9 da miliyan 100 na kuɗin ƙasar Shiling, kwatankwacin dala biliyan 2 da miliyan 500 a duk shekara.
Ta ce wannan ya kai kaso 23 cikin 100 na kasafin kuɗin ƙasar, abin da ke zama wani babban ƙalubale ga ayyukan daƙile cin hanci a ƙasar.
Cin hanci da rashawa wata gagarumar matsala ce da ke addabar gabashin Afirka.
KU KUMA KARANTA: Babban matsalar Najeriya shi ne cin hanci da rashawa – Ndume
Shugaban ƙasar Uganda, Yoweri Musaveni, ya sha nanata alwashin ɗaukar matakan da za su kawo ƙarshen matsalar cin hanci ganin yadda matsalar ta ratsa cikin jami’an gwamnati.
Turwomwe ta ce sashin da ta ke jagoranta ya samu nasarar ƙwato dala miliyan 2 da aka wawushe, inda ta nuna damuwa kan rashin sanya kuɗi a hukumar da take jagoranta.
Wannan kalaman nata ya biyo bayan rahoton shekara-shekara da ake fitarwa na cibiyar bincike kan tabbbatar da ganin an yi ayyukan gwamnati a buɗe babu kumbiya-kumbiya.
Rahoton na zuwa mako guda da shugaban Uganda Yoweri Musaveni ya sanar da yafewa wasu manyan jami’an gwamnati da aka ɗaure shekara 10 saboda kamasu da badaƙalar dala miliyan 1 da miliyan 200.
Musaveni ya yafe musu bayan sun kammala shekara 5 a gidan, abinda ya tunzura ƙungiyoyin fararan hula.