Cikar Yobe shekaru 34: Gwamna Buni ya jaddada aniyar ci gaba da ayyukan raya al’umma

0
139
Cikar Yobe shekaru 34: Gwamna Buni ya jaddada aniyar ci gaba da ayyukan raya al'umma
Gwamna Buni a lokacin da yake hira da manema labarai

Cikar Yobe shekaru 34: Gwamna Buni ya jaddada aniyar ci gaba da ayyukan raya al’umma

Gwamna Mai Mala Buni, CON, ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da ayyukan raya jama’a domin inganta rayuwar al’ummar jihar Yobe. Haka kuma ya buƙaci ɗaukacin jama’a su ci gaba da kasancewa cikin haɗin kai, zaman lafiya da kuma jajircewa wajen gina jihar mai ƙarfi da wadata.

Yayin wata tattaunawa ta musamman da shugabannin kafafen yada labarai na gwamnati a gidan gwamnati Damaturu a ranar Talata, domin bikin tunawa da cikar Yobe shekaru 34 da kafuwa, Gwamna Buni ya bayyana godiyarsa ga Allah Madaukakin Sarki bisa ni’imarSa, jinkai da kariya tun daga ranar da aka kirkiro jihar a ranar 27 ga Agusta, 1991.

Gwamnan ya bayyana wannan rana a matsayin lokaci na murna da kuma nuna godiya bisa “shekaru 34 na jajircewa, ci gaba da hadin kai.” Ya karrama iyayen kafa jihar, shugabannin baya, ma’aikata da kuma al’ummar jihar baki ɗaya da sadaukarwarsu wadda ta taimaka wajen kafa Yobe a matsayin “jihar da ke alfahari da bambancin al’umma, ci gaban ilimi da kuma bunƙasar ɗan Adam.”

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Yobe ta jaddada ƙudirinta na ba da agajin gaggawa ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa

“Hadinkai ce ginshiƙin cigabanmu, kuma bambancinmu shi ne ƙarfinmu mafi girma. Saboda haka ina kira ga daukacin al’ummar Yobe da su ci gaba da tabbatar da zaman lafiya, adalci da ‘yan’uwantaka,” in ji Gwamna Buni.

Ya bayyana irin ci gaban da gwamnatinsa ta samu a ƙarƙashin Tsarin Continuity, Consolidation and Innovation Agenda, wanda yanzu haka ya shiga wa’adi na biyu.

Ya lissafo muhimman ayyuka a Damaturu, ciki har da gina gadar sama ta farko a jihar, kasuwa ta zamani, babban kantin sayar da kayayyaki (shopping mall), tashar mota ta zamani da kuma gina titunan birni da magudanan ruwa.

Ya kara da cewa babu wani karamar hukuma da aka bari a baya wajen cigaban raya kasa. Muhimman ayyukan sun haɗa da gina kasuwanni na zamani, faɗaɗa cibiyoyin kiwon lafiya, kafa sabbin makarantu, shirye-shiryen tallafin noma da kuma gina hanyoyin karkara don bude tattalin arziki, inganta hanyoyin sadarwa da samar da ayyukan yi.

Gwamnan ya kara jaddada cewa gwamnatinsa na mai da hankali kan matasa ta hanyar bayar da tallafin karatu, koyar da sana’o’in dogaro da kai da kuma tallafa musu wajen fara kasuwanci.

Ya yi alkawarin ci gaba da zuba jari a fannin lafiya da ilimi, inda ya bayyana cewa ana sabunta cibiyoyin kiwon lafiya na farko da kayan zamani, sannan ana ci gaba da bayar da magani kyauta ga mata masu juna biyu da kananan yara ‘yan kasa da shekaru biyar.

Haka kuma, Gwamna Buni ya nanata aniyar gwamnatinsa ta bunkasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi musamman ga mata da matasa, a matsayin wani bangare na shiryawa sabbin ƙarni da basu dabaru da kwarewa domin yin nasara a duniyar zamani mai sauyi.

Ya gode sosai ga Majalisar Dokokin Jihar Yobe, bangaren shari’a, mambobin majalisar zartarwa, ma’aikata da al’ummar Yobe baki daya bisa amincewarsu da goyon bayansu. Ya bayyana cewa amanar da aka bashi a 2019, wacce aka sake tabbatar masa da ita a 2023, ita ce babban dalilin da ke kara masa kwarin gwiwa don cigaba da yi wa jihar hidima.

Yayin da yake bayyana Yobe a matsayin “jihar da Allah ya albarkace ta da cigaban ilimi, da daukaka a matakin kasa da na duniya,” Gwamna Buni ya yi kira ga daukacin jama’ar jihar da su kasance abokan tafiya a hangen nesan Continuity, Consolidation and Innovation, domin tabbatar da ci gaba mai dorewa ga al’ummar da ke zuwa.

Wannan tattaunawa ta musamman ta samu halartar Daraktocin Gidan Talabijin na Yobe (YTV), Rediyon Yobe (YBC), Daraktan Bayanai na Ma’aikatar Bayani tare da Focal Person kan Harkokin Dijital da Dabarun Sadarwar.

Leave a Reply