No menu items!

Sample Page Title

Date:

Cibiyar aikin jarida ta IPI ta yi gargadi kan ƙaruwar takura wa kafafen yaɗa labarai a Najeriya

Daga Jameel Lawan Yakasai

Cibiyar Aikin Jarida ta Ƙasa-da-Ƙasa, wato International Press Institute (IPI), wacce ke fafutukar kare ’yancin kafafen yada labarai da kuma tabbatar da walwalar samun bayanai, ta nuna damuwa kan yadda ake samun karuwar matsin lamba da takura wa ’yan jarida a ƙasar nan.

Shugaban IPI Nigeria, Musililu Mojeed, ya yi wannan gargadi ne a wani taron liyafa da ƙungiyar ta shirya a ranar Asabar a Abuja, domin girmama daya daga cikin membobinta, Hajiya Hadiza Hussaina Sani, tsohuwar Daraktar Sashen fasahar zamani ta gidan rediyon ƙasa na VON, wacce ta kammala aikin gwamnati bayan cika shekara 60.

A jawabin sa a wajen taron, Mojeed wanda shi ne Babban Editan Premium Times, ya bayyana damuwarsa kan matakai na baya-bayan nan da suka hada da hana shirin siyasa a kai tsaye a Kano, tare da kama ’yan jarida a jihohin Ekiti da Neja.

KU KUMA KARANTA: Ƙungiyar ‘yan jarida ta ƙasa, ta je ta’aziyyar rasuwar mahaifiyar mawallafin jaridar Neptune Prime

Ya ce: “A jihar Akwa Ibom, gwamnatin jihar ta kori tawagar Channels TV daga Cibiyar ’Yan Jarida da ke fadar gwamnatin Uyo, bayan sun wallafa bidiyon da gwamnan ya tabbatar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

“Haka kuma a jihar Kebbi, wani ɗan jarida mai suna Hassan Mai-Waya Kangiwa an tsare shi bayan ya fallasa sakaci a wani asibiti. A gefe guda kuma, tsohon ma’aikacin ThisDay, Azuka Ogujiuba, an cafke shi tare da cin zarafi saboda aikin jarida kawai.

“Kullum idan ka tashi, sai ka ji an sake tsananta wa kafafen yada labarai,” in ji shi.

Mojeed ya bukaci da ci gaba da fafutuka da gwagwarmaya domin kare ƴancin kafafen yada labarai da kuma bunƙasa aikin jarida mai cin gashin kansa. Ya ce kare ’yancin ’yan jarida da goyon bayan aikin jarida mai zaman kansa muhimmin abu ne a tsarin kafafen labarai na Najeriya.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...