CBN ya soke harajin tura kuɗi ta intanet

CBN ya soke harajin tura kuɗi ta intanet

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya soke sabon harajin tura kuɗi ta intanet da ta bullo da shi a kwanakin baya.

A kwanakin baya ne CBN ya ɓullo da sabon harajin mai suna Harajin Tsaron Intanet, na kashi 0.5% kan duk kuɗin da aka tura ta intanet.

“Muna sanar da bankunan kasuwanci da sauran cibiyoyin haɗar kuɗaɗen cewa, mun janye umarnin da muka bayar na farko kan cirar harajin 0.5% na tsaron intanet daga masu tura kuɗi ta intanet,” in ji CBN.

Janye sabon harajin da ya ja wa babban bankin kakkausar suka daga al’ummar Najeriya na kunshe ne a cikin wata sanarwa da bankin ya fitar mai dauke da sa hannun Chibuzo Efobi, Daraktan Sashe Kula da Tura Kuɗaɗen da kuma Mustafa Haruna, Daraktan Sashen Kula da Tsare-tsaren kuɗaɗe.

KU KUMA KARANTA: CBN ya ba bankuna umarnin saka sabon harajin tura kuɗi

Ana iya tunawa wasu shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci CBN ya soke harajin, wanda majalisar dokoki ta ƙasa ta ƙira da rashin tausaya wa ’yan Najeriya.

Majalisar ta bayyana cewa babban bankin bai fahimci sashen dokar da ya yi amfani da shi wajen ɓullo da sabon harajin ba.

Don haka ne ma majalisar wakilai ta umarci kwamitinta da ya yi wa babban bankin karin haske kan tanadin dokar tsaron intanet.

A baya dai CBN ya bayyana cewa dokar tsaron intanet ce ta tanadi hakan inda za a rika tura kudin zuwa ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro domin gudanarwa.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *