CBN ya ba bankuna umarnin saka sabon harajin tura kuɗi

0
110

Babban Bankin Najeriya CBN ya bayar da umarni ga bankunan Najeriya su soma karɓar harajin kashi 0.5 cikin 100 na duk kuɗin da aka tura a matsayin harajin tsaro na internet.

Babban bankin ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar 6 ga watan Mayun 2024 inda ya buƙaci duka bankunan kasuwanci da waɗanda ba masu karɓar ruwa ba da ƙananan bankuna da ake mu’amula da su ta waya da su bi umarnin wannan doka.

A sanarwar da babban bankin ya fitar, ta ce wannan harajin za a rinƙa tara shi a wani asusu na musamman mai suna National Cybersecurity Fund wanda ofishin Babban Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro zai rinƙa kula da shi.

Babban bankin ya ce nan da mako biyu bayan fitar wannan sanarwa za a soma aiwatar da wannan doka.

KU KUMA KARANTA: Naira ce kuɗin da ya fi samun tagomashi a duniya – Gwamnan CBN

A cikin sanarwar, ya ce wanda zai tura kuɗin za a cire wa haraji, sannan bankin ya tura kuɗin zuwa asusun. Sannan kuma harajin da aka cire zai nuna a asusun kwastoman da aka cire wa kuɗin da taken ‘Cybersecurity Levy’.

Duk da wannan harajin da aka saka, akwai waɗanda bankin ya keɓe da ba za su biya harajin ba.

Daga ciki akwai tura kuɗi domin biyan bashi da tura kuɗi tsakanin asusun ajiyar mutum da ke bankin da yake amfani da shi ko wani banki, sai kuma tura kuɗi tsakanin mutum biyu da ke amfani da banki ɗaya.

Leave a Reply