CBN ta sahalewa ‘yan canji sayen dala dubu 25 a mako guda, saboda bukin kirsimeti

0
7
CBN ta sahalewa ‘yan canji sayen dala dubu 25 a mako guda, saboda bukin kirsimeti

CBN ta sahalewa ‘yan canji sayen dala dubu 25 a mako guda, saboda bukin kirsimeti

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bada sahalewar wucin gadi ga masu sana’ar canjin kudade, su sayi abinda ya kai dala 25, 000 a mako guda daga kasuwar hannayen jarin kasar, tsarin da aka kaddamar a farkon watan da muke ciki.

Tsarin zai yi aiki ne a tsakanin 19 ga watan Disamban 2024, zuwa 30 ga watan Janairun 2025.

KU KUMA KARANTA:NAHCON za ta haramta amfani da dala a aikin hajji, don rage tsadar kuɗin kujera

Sanarwar mai ɗauke da kwana wata 19 ga watan Disamban 2024, da sa hannun T. G Allu, a madadin mai rikon mukamin daraktan sashen kasuwanci da musayar kudade na CBN, ya bayyana cewa an tsara matakin ne domin biyan bukatar musayar kudaden ketare a lokacin hutu.

Sanarwar ta kara da cewa hada-hadar za ta gudana ne akan mizanin musayar da CBN ya tsayar ta NFEM, kuma za’a bukaci masu sana’ar musayar kudaden su tsaya a kan ribar da bata zarta kaso 1 cikin 100 ba wajen sayar da kudaden musayar ga masu bukata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here