No menu items!

Sample Page Title

Date:

Babban burin Turkiyya shi ne samun “cikakken ƴanci a ɓangaren makamashi,” kamar yadda Shugaba Erdogan ya bayyana.

“Babban burinmu shi ne samun cikakken ƴanci a ɓangaren makamashi. Mun kuduri aniyar aiwatar da ayyukan da za su tabbatar da ɗorewar makamashin Turkiyya,” kamar yadda Erdogan ya bayyana a jawabinsa na ranar Asabar a yayin wani taro da da Turkiyya ta shirya a lardin Zonguldak na Turkiyya da ke gaɓar Tekun Bahar Rum.

Erdogan ya ƙara da cewa adadin da rijiyar mai ta Tsaunin Gabar ke samarwa a kullum wadda ke a lardin Sirnak ya haura sama da ganga 35,000 a duk rana.

“Muna son a duk rana abin da za a samu a Gabar ya kai ganga 100,000 a duk rana zuwa ƙarshen 2024,” kamar yadda ya ƙara da cewa.

KU KUMA KARANTA: Shugaba Erdogan ya sha alwashin taimaka wa waɗanda girgizar ƙasa ta shafa a watan Fabrairun 2023 a Turkiyya

Erdogan ya kuma bayyana fatan sanar da sabon labari mai dadi a cikin lokaci mai zuwa game da man fetur, hakar ma’adinai, da iskar gas, yana mai karawa da cewa: “Ba za mu sake ba da damar hana amfani da albarkatun Turkiyya waɗanda ke ƙarƙashin ƙasa da na doron ƙasa ba.”

Tun daga 2020, Turkiyya ta haɓaka aikin da take yi na haƙo mai da iskar gas, haka kuma waɗannan ayyukan sun jawo an sake gano wasu albarkatun ƙasa a yankin Gabar da ke lardin Sirnak.

Matsayin da aka samu na samar da man fetur da sabbin ma’adinan ya kawo ƙasar kusa da burinta na samun ‘yancin kai na makamashi.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...