Bukukuwan Idin babbar Sallah: Al’umma su bawa ‘yan sanda haɗin kai – Kwamishinan ‘yan sanda

0
266

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Yobe, ya yi ƙira ga al’ummar jihar Yobe da su bawa ‘yan sanda haɗin kai a bukukuwan babbar sallah. Ya yi wannan ƙiran ne a wata takarda da kakakin ‘yan sandan jihar Yobe Dungus Abdulkarim ya fitar a ranar Talata. Ya ce wannan shi ne nanata ƙudurin rundunar ‘yan sandan jihar Yobe na tabbatar da tsaron al’ummar musulmi a duk filin Idi na jihar da kuma samar da yanayi na gudanar da bukukuwan Sallah lafiya a jihar.

A yau Talata ne ya yiwa hafsoshi da jami’an rundunar bayani kan matakan da suka dace gabanin Sallah.

Kwamishinan ‘yan sanda, CP Garba Ahmed, ya umarci jami’an da su kasance masu ƙwazo da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu tare da jaddada cewa masu yin ɓarna da rashin jin daɗin jama’a da ke son yin amfani da wannan biki wajen aikata miyagun laifuka ba za su samu wurin yin hakan ba, domin kuwa rundunar ta tura jami’ai da kayan aiki wajen samar da tsaro kafin bukukuwan Sallah da kuma bayan bukukuwan Sallah.

KU KUMA KARANTA: Babbar Sallah: Hukumar NSCDC ta tura jami’ai 2,500 a Kano

Don haka kwamishinan ya yi ƙira ga al’ummar jihar Yobe da su bawa ‘yan sanda da jami’an tsaro haɗin kai ta hanyar bayar da bayanai masu amfani ga ofishin ‘yan sanda ko jami’an tsaro mafi kusa da kai rahoton duk wani mutum (wani), motsi, mota, abin hawa.

A halin da ake ciki kuma, lura da illolin da masu ababen hawa ke yi na tuƙin ganganci a lokacin bukukuwan Sallah a baya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da ba su ji ba, ba su gani ba.

An shawarci masu ababen hawa da su kasance masu bin doka da oda, da bin ƙa’idojin zirga-zirga, guje wa tuƙin ganganci da bayar da gudumawa wajen samar da zaman lafiya a jihar.

Don haka Kwamishinan ’yan sandan ya yi wa al’ummar Musulmin Jihar Barka da Sallah, da fatan za a yi bukukuwan Sallah lafiya.

Leave a Reply