Buhun Siminti: Mun so farashin ya tsaya a yadda yake, amma diloli suka ƙi – BUA

0
24
Buhun Siminti: Mun so farashin ya tsaya a yadda yake, amma diloli suka ƙi - BUA

Buhun Siminti: Mun so farashin ya tsaya a yadda yake, amma diloli suka ƙi – BUA

Shugaban kamfanin BUA Cement Plc, Abdulsamad Rabiu, ya bayyana yadda diloli suka riƙa yin ƙafar-ungulu a shirin kamfaninsa na sayar da kowane buhun siminta a kan N 3,500 a bara.

Da yake jawabi a wurin taron shekara-shekara na kamfaninsa a Abuja ranar Alhamis, Abdulsamad Rabiu ya zalamar da diloli suka riƙa yi ta neman ƙazamar riba ce ta sa suka dinga ƙara kuɗi a kan farashin simintin.

A cewarsa, “Diloli da dama sun yi amfani da damar da muka bayar ta karya farashin siminti don cim ma manufarsu mara kyau. Maimakon su ƙara riba kaɗan a kan farashin da muka sayar musu, sai suka riƙa ninka farashinsa.”

KU KUMA KARANTA:Tinubu ya umarci Ɗangote da BUA su rage farashin siminti

“Wasu daga cikinsu sun riƙa sayar da kowane buhu ɗaya na siminti a kan N7,000 zuwa N8,000. Ba ƙaramin kuɗi suka samu ba. Ina tsammani mun sayar da fiye da tan miliyan ɗaya a kan N3,500 kafin mu fahimci abin da dilolin suke yi,” in ji shugaban kamfanin BUA.

Ya ce, “Mun so farashin ya tsaya a yadda yake amma diloli suka ƙi. Don haka, babu yadda za mu iya ci gaba da sayar da shi a kan wancan farashin domin kuwa tamkar diloli kaɗai muke bai wa tallafi.”

Abdulsamad Rabiu ya ƙara da cewa karyewar farashin Naira da cire tallafin man fetur su ma sun taimaka wajen rashin ɗorewar shirin nasa na karya farashin siminti.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here