Buhari ya sake naɗa Dabiri-Erewa a matsayin babban jami’ar hukumar NiDCOM

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya buƙaci majalisar dattawa ta tabbatar da sake naɗa Abike Dabiri-Erewa a matsayin babbar jami’ar hukumar ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje, NIDCOM.

Buƙatar Buhari na ƙunshe ne a cikin wata wasiƙa da ya aike wa shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan kuma aka karanta a zauren majalisa ranar Talata.

Buhari a cikin wasiƙar ya ce naɗin ya kasance daidai da tanadin sashe na ƙ karamin sashe na 2 na dokar kafa NiDCOM na 2017.

Haka zalika, shugaba Buhari a wata wasiƙa da ya aike wa shugaban majalisar dattawan, ya nemi a tabbatar da sunayen mutane shida da aka naɗa domin naɗa su a matsayin kwamishinonin tattara kuɗaɗen shiga na tarayya da hukumar kula da kasafin kuɗi.

Buhari ya ce buƙatar ta biyo bayan tanadin sashe na 154 ƙaramin sashe na 1 na kundin tsarin mulkin ƙasar na shekarar 1999.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Najeriya ta naɗa Farfesa Mahmud shugaban asibitin ƙasa da ke Abuja

Waɗanda aka zaɓa za su cike guraben da ake da su a wasu jihohi.

Waɗanda aka naɗa sun haɗa da Ayogu Eze (Enugu), Peter Opara (Imo), Hawa Umaru Aliyu (Jigawa). Sauran sun haɗa da Rekiya Haruna (Kebbi), Ismaila Mohammed Agaka (Kwara) da Kolawole Daniel Abimbola (Oyo).


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *