Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya dawo Abuja bayan ziyarar aiki ta kwanaki takwas a ƙasar Saudiyya, inda ya kuma gudanar da aikin Umrah.
Shugaban na Najeriya ya bar Saudiyya a filin jirgin sama na Sarki Abdulaziz na Jeddah a ƙasar Saudiyya ranar Laraba.
kamfanin dillacin labran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa jami’an gwamnatin Saudiyya da shugabannin masaratun gargajiya daga Najeriya da kuma wasu manyan ma’aikatan ofishin jakadancin Najeriya da ke ƙasar sun je filin jirgin domin bankwana da shugaban.
KU KUMA KARANTA: Buhari ya isa birnin Madina don gudanar da umara da ziyarar aiki
Shugaban ya samu nasarar gudanar da aikin Umra ne, cikin tsauraran matakan tsaro, bayan da ya isa babban masallacin Juma’a na Makkah daga Madina da safiyar Alhamis.
NAN ta ruwaito cewa shugaban ƙasar ya samu jagoranci tare da ‘yan tawagarsa da kuma wasu Malaman addini daga shiyyoyin siyasa shida na ƙasar ƙarƙashin wata tawaga daga fadar shugaban ƙasa mai kula da harkokin babban masallacin juma’a a wajen gudanar da ibadar.
A baya dai shugaban na Najeriya ya ziyarci wasu wuraren ibada na tarihi a Madina a ranakun Talata da Laraba kafin ya wuce Makkah domin yin aikin Umrah.
Shugaban ya kuma samu bayanai kan abubuwan da ke faruwa a gida daga wasu jami’an gwamnati da suka haɗa da gwamnonin jihohin Borno da Yobe.
Haka kuma a birnin Makkah, shugaba Buhari ya karɓi baƙuncin wasu malaman addini wajen buɗa baki. Sarakunan Kano da Bichi na Jihar Kano, Aminu Ado Bayero da Alhaji Nasiru Ado Bayero da suka yi jawabi bayan taron duk sun ce ƙasa ɗaya ce kaɗai za ta iya ci gaba da cimma burinta.
Malaman addinin da suka halarci taron sun haɗa da Abubakar Sulaiman, babban limamin fadar Aso Rock Villa, Sheikh Al-Kanawi Alhassan Ahmed, Dr. Bashir Umar, Muhammad Kamaluddeen Lemu da Nuruddeen Danesi Asunogie.
Sauran sun haɗa da Ibrahim Kasuwar Magani, Farfesa Shehu Galadanchi, Abdulrasheed Adiatu, Sheikh Haroun Ogbonnia Ajah da Bala Lau. Shugaban ya kuma gana da Otaru na Auchi, Dr. Aliru Momoh, Sarkin Lafiya, Justice Sidi Mamman Bage, Sarkin Bauchi, Rilwan Adamu Sulaiman, Akadiri Saliu Momoh, Abdulfatah Chimaeze Emetumah, Fatima Ijeoma Emetumah da Isa Sanusi Bayero.
An gudanar da addu’o’in samun zaman lafiya a ƙasar nan, ya kuma kawo ƙarshen wa’adin mulkin shugaban ƙasa cikin nasara da kuma samun nasarar gwamnati mai zuwa.
A baya dai Shugaba Buhari ya ziyarci Masallacin Annabi da ke Madina tare da yin Sallah. Ya kuma gana da dattijo, mai taimakon jama’a kuma uban gidan Dantata, Aminu Ɗantata, a garin Makkah inda ya sake bayyana ta’aziyyarsa bisa rasuwar matarsa Rabi’u Ɗantata.
NAN ta ruwaito cewa ɗan kasuwan ɗan asalin Kano ya rasa matarsa Rabi Ɗantata a wata cibiyar kula da lafiya a ƙasar Saudiyya a ranar 9 ga watan Afrilu.