Buhari ya ƙaddamar da shirin shekarar 2050 don samar da ayyukan yi miliyan 165 ga ‘yan Najeriya

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da ajandar shiri a Najeriya na shekarar 2050 da nufin ƙara haɓaka tattalin arziƙin cikin gida da kashi bakwai cikin ɗari da kuma samar da sabbin ayyuka miliyan 165 a faɗin ƙasar nan.

An ƙaddamar da taron ne jim kaɗan kafin a fara taron majalisar zartarwa ta tarayya na wannan mako a zauren majalisar da ke fadar shugaban ƙasa, Abuja.

Hakan na zuwa ne kimanin makonni bakwai bayan da FEC ta amince da daftarin manufofin a ranar 15 ga watan Maris da kusan watanni uku bayan Majalisar Tattalin Arziƙin Ƙasa ta amince da Ajandar.

A nasa jawabin, shugaba Buhari ya tabbatar da cewa, hangen nesan ya samo asali ne daga tsarin tattalin arziƙi mai tsauri na ilimi don samar da ci gaba mai ɗorewa nan da shekarar 2050.

KU KUMA KARANTA: Buhari ya taya ‘yan jarida murnar zagayowar ranar ‘yancin ‘yan jarida ta duniya

Ya kuma bayyana imanin cewa takardar wadda ta yi nufin ƙara kuɗin shiga ga kowane ɗan Najeriya zuwa dala 33,328 a duk shekara.

Za a sanya shi cikin manyan ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziƙi a duniya nan da shekarar 2050, za su kasance masu amfani ga gwamnatoci masu zuwa.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *