Buhari ya ƙaddamar da gidajen naira biliyan 9.5 a Zuba

A ranar talata ne shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da rukunin gidaje na tarayya da ke Zuba, babban birnin tarayya, (FCT).

Gidan wanda ke kan fili mai faɗin hekta 18.5, ya ƙunshi gidaje 748, kuma hukumar kula da gidaje ta tarayya, (FHA) ce ta gina shi.

Da yake jawabi yayin taron, Shugaban ya bayyana cewa, Gidan na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin tarayya na daƙile fatara da samar da matsuguni ga al’umma.

Buhari ya ce aikin wanda ya ba da gudummawar ayyuka da dama a yayin gine-gine wani ɓangare ne na ƙudurin sa na kyautata rayuwa ga ‘yan ƙasa.

“Samar da gidaje yana ɗaya daga cikin ma’aunin Talauci na ‘Multidimensional Poverty Index’ wanda ke ƙalubalantar mutanenmu kuma kammala aikin zai samar da mafita ga waɗanda suka amfana.

KU KUMA KARANTA: Kungiyar Noman Zamani Ta NAMCON Ta Kaddamar Da Shugabannin Reshen Jihar Katsina

Sabbin masu gidajen da suka ci gajiyar wannan kadarorin za su ɗauki mataki kan matakin wadata daga talauci.” Yayin da ya yarda cewa gwamnati na da sauran abubuwan da za ta yi wa ‘yan Najeriya da dama su mallaki gidaje, ya ce gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen kammala ayyukan gidaje kafin ya bar ofis.

“Daya daga cikin matakan da muka ɗauka da sane don kai hari kan talauci, samar da wadata da bunƙasa tattalin arziƙinmu shi ne yadda muke samar da ababen more rayuwa a faɗin ƙasar. Alƙawarin mu na canji yana cika ga masu gida”.

A yayin da yake taya sabbin masu gidaje a yankin, ya buƙace su da su zauna lafiya tare da haɗa kai da hukumar ta FHA domin kawo ci gaba mai ɗorewa a yankin.

A nasa ɓangaren, ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ya ce an amince da tallafin aikin ne a shekarar 2018. Fashola ya ce sama da ma’aikata 13,000 ne suka ci gajiyar aikin kai tsaye da kuma a kaikaice daga ‘yan kwangila 75.

Ya ce masu cin gajiyar gidajen ya haɗa da waɗanda suka biya ta hanyar jinginar gidaje, biyan kuɗin-ɗaya da kuma na haya.

“Kammala aikin yana nuni da ƙudurin mu na cewa ba za mu bar ayyukan da aka yi watsi da su ba. Gine-ginen ya bai wa ’yan Najeriya aikin yi sun haɗa da masu sana’ar hannu da kuma masu sayar da abinci waɗanda ke yawan zuwa neman kuɗi domin su da iyalansu.”

Manajan Darakta na FHA, Ashiru Ashafa, ya ce hukumar ta ɗauki nauyin aikin ne ta hanyar tallafin biliyan 7.5 daga gwamnati da kuma biliyan 2 daga kuɗaɗen shiga da take samu a cikin gida.

Ya ce gidan na da benaye mai ɗakuna 1,2 da 3 da kuma fili mai ɗakuna 3, ya ƙara da cewa nan ba da daɗewa ba FHA za ta ƙaddamar da rukunin gidaje 336 a Bwari.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *