Buhari, Kwankwaso, Atiku sun jajanta wa al’ummar Maiduguri

0
108
Buhari, Kwankwaso, Atiku sun jajanta wa al’ummar Maiduguri

Buhari, Kwankwaso, Atiku sun jajanta wa al’ummar Maiduguri

Tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso sun jajanta wa al’umar jihar Borno bisa ibtila’in ambaliyar ruwa da ta afka wa birnin Maiduguri.

Da tsakar daren Litinin wayewar garin Talata ambaliyar ruwa ta malale wasu yankunan babban birnin na Borno bayan da wani sashe na madatsar ruwan Alau ya fashe.

Tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya nuna alhininsa dangane da wannan al’amari yana mai fatan hukumomin agaji za su taimaka wajen saukaka raɗaɗin ambaliyar.

“Tunaninmu da addu’oi’nmu suna tare da waɗanda wannan ibtila’i ya shafa.” Buhari ya ce cikin wata sanarwa da kakakinsa Malam Garba Shehu ya fitar.

Shi mai tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya mika saƙon jajensa.

KU KUMA KARANTA: Ambaliyar ruwa a Maiduguri ta shafe wasu sassan garin (Bidiyo)

“Zuciyarmu tana tare da al’umar Maiduguri da gwamnatin jihar Borno yayın da suke fama da wannan babbar jarabawa da ta shafi tattalin arziki” Atiku ya ce cikin wata sanarwa da ya fitar a kafafen sada zumunta.

Ya ƙara da cewa, “ina kuma ƙira ga hukumomin ba da agaji da su gaggauta kai ɗauki don sauƙaƙawa jama’a wannan bala’i.”

A nasa ɓangaren, tsohon gwamnan Kano Kwankwaso ya ce, “Ina ƙira ga hukumomi da dukkan waɗanda za su iya taimakawa da su kai wa jama’a ɗauki.”

“Tunaninmu da addu’inmu na tare da gwamnatin jihar Borno da al’umominta yayin da suke fuskantar wannan mawuyacin hali.’ Kwankwaso ya ƙara da cewa.

Leave a Reply