Wasu kwamandoji da jami’an tsaron sa-kai na Civilian JTF sun rasu bayan da suka taka bom da ake zargin na mayaƙan Boko Haram ne a Jihar Borno.
Dakarun na Civilian JTF sun gamu da ajalinsu a sakamakon taka nakiyar ce a kusa da ƙauyen Ndufu da ke ƙaramar hukumar Ngala a ranar Alhamis.
Wata majiyar tsaro ta shaida mana cewa, “Babban Kwamandan Gambarou, Bukar Goni, da Kwamandan yankin Ngala, Malam Cede na cikin mutum shida da ke cikin motar kuma dukkansu sun rasu.”
KU KUMA KARANTA: Sojoji da DSS sun daƙile yunkurin Boko Haram na kai hari a Kano
Majiyar ta shaida ce motar sintirin da jami’an tsaron suke ciki ce ta taka bom din da aka binne a gefen hanya, a yayin da suke gudanar da sintiri a Ndufu.
Ta ce jami’an tsaron sun bar garin Ngala da misalinn karfe 3 na rana zuwa Ndufu, inda “kafin su shiga garin Duhu, motarsu ta tarwatse bayan da ta taka bom ɗin, dukkansu suka rasu.”
Wakilinmu ya yi ƙoƙarin samun ƙarin haske daga ’yan sanda, sai dai ko da ya ƙira kakakin ’yan sandan Jihar Borno, jami’in bai amsa ƙiran ba.