Boko Haram sun yi wa tawagar sojoji kwanton ɓauna a Borno, sun kashe soja, sun ƙona fasinjoji da ransu

0
350

Wasu ‘yan ta’addan da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne sun yi wa motocin jami’an tsaro da ke rakiya a kan hanyar Gwoza- Limankara-Uvaha, inda suka kashe soja guda a nan take.

Kazalika, wata motar sintiri ta jami’an tsaro ta ƙone ƙurmus, an kuma ƙona motocin kasuwanci guda biyar tare da fasinjojin su a ciki, don haka har yanzu ba a ga gawarwaki goma sha biyu ba.

Majiyoyin tsaro na cikin gida da na tsaro sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 5 na yamma a lokacin da sojoji da civilian JTF ke bai wa fasinjojin da ke tafiya zuwa Goza, ƙaramar hukumar Askira-Uba a Borno da Arewacin jihar Adamawa mafaka.

“GOC tana wurin da aka kai harin. An kashe soja ɗaya da fasinjoji da dama a harin, sannan an ƙona motoci biyar ciki har da wata motar soji tare da fasinjojin da ke ciki.

KU KUMA KARANTA: Boko Haram a Borno sun yi garkuwa da mata bakwai, sun kashe biyar

‘Yan ta’addan sun yi awon gaba da wasu matafiya fasinjoji amma sun sake su da yammacin yau,” kamar yadda wata majiyar soja ta shaida wa wannan jarida. Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, wanda shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce an yi musu kwanton ɓauna ne da yammacin ranar Asabar.

Ya ce yawaitar kashe-kashe a yankin Goza ya yi ƙamari a ‘yan kwanakin nan. “Yana faruwa a kowace rana.

Don haka muna ƙira ga sojoji da su kai wannan yaƙi zuwa inda ’yan ta da ƙayar baya suke domin duk mun san inda suke.

“Yanzu manoma na fargabar zuwa girbi gonakinsu, don haka lokaci ya yi da ya kamata sojoji su jagoranci farar hula da ke da niyyar shiga yaƙin, a samar musu da kayan aiki don ƙwato yankin,” in ji Ndume.

Leave a Reply