Wasu da ake zargin ‘yan ƙungiyar Boko Haram ne sun kashe aƙalla mutane 15 a hare-haren da suka kai kan wasu ƙauyuka biyu a ƙaramar hukumar Jere ta jihar Borno.
Kamar yadda rahoton Daily Trust ta ruwaito, ‘yan ta’addan sun kai farmaki ƙauyen Ƙofa ne da tsakar dare inda suka fara harbe-harbe ba da daɗewa ba, wanda har zuwa safiyar Juma’a.
An tattaro cewa maharan sun kuma kai hari a ƙauyukan Molai Kura da Molai Gana inda suka yi ta yanka mutane da ba a tantance adadinsu ba.
KU KUMA KARANTA: Yadda ‘yan Boko Haram suka yiwa masunta 29 kisan gilla, suka jikkata 9 a Gamborun Ngala
Lamarin dai ya sa mazauna yankin da dama sun ƙauracewa gidajensu zuwa wani daji da ke kusa.
Wani jigo a ƙungiyar ’yan banga, Bukar Ali-Musty, ya shaida wa jaridar cewa manoman na aikin gonakinsu ne a kusa da Molai, da ke wajen birnin Maiduguri, a ranar Alhamis ɗin da ta gabata, inda ‘yan tada ƙayar bayan suka kai musu hari suka sare kawunansu.
“Aƙalla gawarwaki 15 ne aka kwashe a safiyar yau, an kai hare-haren ne jiya (Alhamis).
“An sare kan manoma bakwai a lokacin da suke aikin gonakinsu, sannan maharan sun kuma yanka wuya ga wasu fararen hula takwas da ba su da illa a gidajensu,” in ji shi.
Wani memba a ƙungiyar ‘civilian JTF’ da ke cikin tawagar da aka kwashe, ya nuna damuwarsa kan hare-haren, yana mai cewa dole ne duk masu ruwa da tsaki su farka don ganin ba a ci gaba da faruwa ba.
“Abin takaici ne ci gaba idan aka yi la’akari da ci gaban da muka samu a cikin watanni ba tare da an kai wa al’umma hari ba.
“Ina can da safe. Ba zan iya tunanin ganin an yanka ’yan uwana kamar rago ba.
Dukkanin gawarwakin da muka ƙwato an same su ne a cikin kwance cikin jini, kuma ina ganin dukkanmu muna buƙatar mu tashi tsaye domin tunkarar wannan maƙiyin zaman lafiya,” inji majiyar.
[…] KU KUMA KARANTA: Boko Haram sun kashe manoma 15 a jihar Borno […]