No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun kashe Sheikh Baba Goni Muktar Malumti, babban limamin masallacin Jumu’a na tsakiyar garin Benisheikh, hedikwatar ƙaramar hukumar Kaga a jihar Borno.

An tattaro cewa ‘yan ta’addan da ke cikin wata mota Volkswagen sun kai farmaki gidan limamin da ke Malamti, a wajen garin Benisheikh da misalin ƙarfe 12:30 na safiyar ranar Litinin, 30 ga Oktoba, 2023.

‘Yan ta’addan sun kuma ƙona wasu litattafai na marigayin. Imam kafin rasuwarsa ya kasance sanannen malamin addinin musulunci.

A cewar wata majiyar rundunar haɗin gwiwa ta Civilian Task Force, yanayin farmakin ya kasance na masu tada ƙayar baya ne.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...