No menu items!

Sample Page Title

Date:

Birtaniya ta bayyana shirinta na tallafa wa kasar Ukraine da tallafi mafi girma a yaƙin da take yi da ƙasar Rasha.

Firayim Minista Rishi Sunak ya bayar da bayani kan tallafin na fam miliyan 500 (kimanin dalar Amurka miliyan 620m) yayin wata ziyara a Poland.

Ukraine dai ta yi ƙira da a ƙara ƙaimi taimaka mata a daidai lokacin da dakarun Rasha suka fara kai farmaki a fagen daga tare da ƙara kai hare-hare ta sama.

Birtaniya ta bayyana hakan ne a daidai lokacin da Amurka ke ƙoƙarin tura wani tallafin  kimanin Dala biliyan 60.

Kuɗaɗen za su kai jimillar taimakon sojan Burtaniya da za a bai wa Ukraine zuwa fam biliyan 3 (dala biliyan 3.71) a cikin kasafin kuɗin wannan shekarar, in ji gwamnatin Burtaniya.

KU KUMA KARANTA: Amurka ta gargaɗi Nijar kan alaƙarta da Rasha da Iran

Sabon ƙunshin tallafin zai ba da dmar samar da harsasai, matakan tsaro na sama, jirage marasa matuƙa da tallafin injiniyoyi.

Gwamnati ta ce “za a siyo jiragen marasa matuƙa a Burtaniya kuma kuɗaɗen za su taimaka wajen bunƙasa samar da tsaro na cikin gida”.

Abin da Burtaniya ke ƙira “ƙunshin kayan aiki mafi girma da aka taɓa yi” zai kuma haɗa da jiragen ruwa 60 da sama da makamai masu linzami 1,600 da makami mai linzami da kuma makamin da ake harba shi a iska na dogon zango da madaidaitan makamai masu linzami.

Fiye da motoci 400 da suka haɗa da 162 masu sulke, za a kuma kai su da harsashi miliyan 4 na ƙananan makamai.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...