No menu items!

Sample Page Title

Date:

Shugaban Amurka Joe Biden ya shaida wa takwaransa na Masar Abdel Fattah el Sisi ta wayar tarho cewa ƙasarsa ba za ta amince a tursasa wa Falasɗinawa fita daga yankin Gaza da aka mamaye ba, ko kuma Gabar Yammacin Kogin Jirdan, kamar yadda wata sanarwa daga Fadar White House ta bayyana.

“Shugaban ƙasa yana mai tabbatar da shirinsa na kafa ƙasar Falasɗinawa da kuma jaddada muhimmancin rawar da Masar za ta taka wajen ganin an bi waɗannan ƙa’idoji,” in ji White House.

Sanarwar ta ƙara da cewa Shugaba Biden ya bayyana jin daɗinsa “game da ƙoƙarin Masar na ƙulla yarjejeniyar sakin mutanen da Hamas ta kama tare da tsagaita wuta a Gaza.”

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...