No menu items!

Sample Page Title

Date:

Alhaji Ibrahim Oyinlade, babban limamin unguwar Uso dake ƙaramar hukumar Owo ta jihar Ondo, ya samu ‘yanci daga hannun masu garkuwa da mutane.

Sakin sa na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan masu garkuwa da mutanen sun nemi iyalansa da su biya shi kuɗin fansa naira miliyan 10.

Duk da haka, babu tabbas ko dangin sun biya kuɗin fansa ko kuma malamin ya sami ‘yanci da kansa.

Rahotanni sun bayyana cewa malamin yana aiki ne a gonarsa lokacin da maharan suka mamaye harabar inda suka tafi da shi ranar asabar.

KU KUMA KARANTA : Sai an bamu miliyan 10 za mu sako limamin Ondo – Masu garkuwa da mutane

“Kodayake masu garkuwan sun tuntuɓi ‘yan uwa da safiyar yau (Lahadi) inda suka buƙaci Naira miliyan 10, an sako shi da yammacin yau” in ji wata majiya daga dangin.

Majiyar dangin ba ta bayyana ko an biya kuɗin fansa kafin a sako malamin ba.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

1 COMMENT

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...