Bayan ya rage farashin siminti, kamfanin BUA ya ƙara farashin sukari, fulawa, da spaghetti

0
406

A wani yunƙuri na ban mamaki, kamfanin BUA ya ƙara farashin sukari, fulawa, da spaghetti, bayan sanar da rage farashin siminti.

Alfijir labarai ta rawaito cewa bayan wani bincike da ta gudanar a kasuwar Kano ya nuna cewa kamfanin na BUA ya ƙara farashin sukari da fulawa da kuma taliya a shahararriyar kasuwar Singa ta Kano, Yanzu haka ana sayar da sukari kan naira 47,500 kan kowanne buhu wani wajen ma yafi haka, spaghetti kan katan naira 9,000, da buhun fulawa a kan naira 34,500.

Wani dillalin kayayyakin na BUA a Kano ya ce ƙarin farashin ya biyo bayan da kamfanin ya sanar da rage farashin siminti.

“Mun lura da ƙaruwa a cikin makon nan, farashin buhun gari yanzu ya haura N34,500 saɓanin naira 31,000 zuwa N32,000 da aka sayar a makon da ya gabata, an ƙara kusan naira 2,000 a buhun fulawa a farashin kamfani.” inji dillalin.

KU KUMA KARANTA: Kamfanin BUA ya karya farashin buhun siminti zuwa dubu uku da ɗari biyar

“Akan sukari babu wani farashi mai inganci amma ana sayar dashi har zuwa Naira 48,000 zuwa sama.

A satin da ya gabata ana sayar da shi akan kuɗi naira 44,500 zuwa naira 45,000, wani yace min yana sayar da shi akan Naira 46,500.

Dillalin ya ce “an sanar da mu game da ƙarin kuɗin da aka yi a wannan makon, yawanci suna tattaunawa damu ta hanyar wayar tarho.

Ina kuma so in gaya muku cewa duk waɗannan farashin, daga kamfani ne,” inji dillalin.

Leave a Reply