Ƙungiyar ƙwadagon ta dakatar da zanga-zangar da ta ke yi a faɗin ƙasar bayan ganawa da shugaban ƙasa Bola Tinubu a yammacin ranar Laraba a fadar gwamnati da ke Abuja.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Dele Alake, mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan ayyuka na musamman, sadarwa da dabaru ya fitar a Abuja ranar Laraba.
Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya NLC, ya samu jagorancin shugabanta, Joe Ajaero, yayin da Festus Usifo ya jagoranci ƙungiyar ‘yan kasuwa TUC.
KU KUMA KARANTA: ‘Yan ƙwadago a Najeriya sun bai wa Majalisa wa’adi ko su shiga yajin aiki
Sakamakon tattaunawa mai ma’ana da gaskiya da Mista Tinubu da kuma ƙwarin gwiwar da suke da shi na ƙarfafa yin la’akari a fili da gaskiya ga dukkan batutuwan da aka gabatar, shugabannin ƙwadagon sun ce sun yanke shawarar dakatar da zanga-zangar.
Sun zaɓi ci gaba da hulɗa mai kyau da gwamnati domin warware duk wasu batutuwan da suka shafi aiki da kuma ‘yan Najeriya baki ɗaya.
Mista Tinubu ya bai wa shugabannin ƙwadagon alƙawarin cewa matatar mai ta Fatakwal za ta fara aiki a watan Disamba bayan kammala kwangilar gyaran da ake yi tsakanin kamfanin NNPC da na ƙasar Italiya, Maire Tecnimont SpA.
Shugaban ya kuma tabbatar wa da shugabannin ƙwadagon cewa zai ci gaba da yin aiki don amfanin Najeriya, yayin da ya roƙe su da su haɗa kai da shi domin a haifi ƙasa mai inganci da tattalin arziƙi.