Barau Jibrin ya fi Ganduje hannu a haddasa rikicin siyasar Kano – Jaafar Jaafar
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Shahararren ɗan jaridar nan, kuma mamallakin jaridar DAILY NIGERIAN, Jaafar Jaafar ya zargi Mataimakin Shugaban Malissar Dattawa, Sanata Barau Jibrin da hannu cikin fitintinu masu nasaba da siyasa da ke faruwa a Jihar Kano.
Jaafar Jaafar ya baiyana hakan ne a cikin shirin “Fashin Baƙi” da su ke gabatarwa a duk ranar Lahadi tare da Lauya, Abdu Bulama Bukarti, Lauya Abba Hikima , Dan jarida Nasiru Zango da kuma Naziru Mika’il.
A cewar Jaafar “Mutane da yawa su na tunanin Ganduje ne, Wallahi Barau ya fi hannu a wannan masifar. Su na shirya gidoga ne su faɗa wa shugaban ƙasa cewa mutane sun dawo daga rakiyar gwamnati mai ci a Jihar Kano ba sa son ta idan ta yi taro aka gani da jama’a da yawa ya soke wannan zargi.
KU KUMA KARANTA:Ina ƙira ga ‘yan Najeriya a ƙara haƙuri da Tinubu – Ganduje
“Kusan duk wannan abubuwan da ake ƙullawa Wallahi da hannunsu. Ko ɗansanda za a kawo Kano sai wanda suke so wanda zai kare muradunsu.
“Irin wannan bai kamata ba. Ko takarar gwamna mutum zai yi, bai kamata ya kasaara al’umma ba. Irin wannan bai dace ba, ba kuma kishin jiha da al’umma ba ne,” in ji Jaafar Jaafar