No menu items!

Sample Page Title

Date:

Bankin Musulunci na Raya Ci gaban Tattalin Arziƙi (IsDB) ya amince da bayar da dala miliyan 418 domin ayyukan ci gaba a Tajikistan da Benin, Ivory coast da Turkiyya.

Kwamitin zartarwa na bankin ya sahale da aiwatar da ayyukan huɗu yayin taronsa karo na 355 l, wanda ya mayar da hankali kan ci gaban zamantakewa da tattalin arziki.

Bankin ya sanar a taronsa na shekara-shekara, wanda ya zo daidai da cikarsa shekaru 50, a babban birnin Saudiyya, Riyadh.

Tajikistan za ta samu dala miliyan 150 don gina tashar lantarki ta Rogun Lot-4, don samar da makamashin lantarki mai tsafta da ƙasar za ta iya dogara a kai.

Benin za ta samu Euro miliyan 60.6 (dala miliyan 65) don ci gaban harkar noman rogo, wanda zai haɓaka wadatar abinci da samar da kuɗaɗe ga al’ummar ƙasar.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Kebbi ya ba da tallafin naira miliyan 309 a ɗaliban da ke karatu a ƙasashen waje

Shirin zai kuma inganta tattalin arziƙi da ƙarfin sarrafa kayan noma, da shigowar fannin kamfanoni masu zaman kansu a harkar sarrafa rogo, dankali, da doya.

Ivory coast za ta samu Euro miliyan 70.56 (dala miliyan 75.5) na kuɗaɗe don haɓaka fannin noman rogo, don wadatar da ƙasa da abinci, da ɗaukaka tattalin arziƙi da samar da kuɗin shiga ga mutane ta hanyar noman rogo, da sarrafa shi da haɗin gwiwar kamfanoni masu zaman kansu.

Kwamitin ya amince da Euro miliyan 120 (dala miliyan 128.5) ga Turkiyya don aikin babban titin Nakkas-Basaksehir, wanda zai kasance wani yanki na babban titin Arewacin Marmara ƙarƙashin shirin gwamnatin ƙasar.

Bankin ya ce game da aikin ci gaba a Turkiyya, “Babbar manufar aikin shi ne samar da wata mashiga, ƙari kan titin tsallaka Bosphorus, don rage yawan ababen hawa da tsaiko, da rage lokacin tafiya, da yawan fitar da iskar gas mai gurɓata muhalli”.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...