Bankin Duniya ya yi hasashen bunƙasar tattalin arziƙin Najeriya a 2025

0
27
Bankin Duniya ya yi hasashen bunƙasar tattalin arziƙin Najeriya a 2025

Bankin Duniya ya yi hasashen bunƙasar tattalin arziƙin Najeriya a 2025

Bankin duniya ya yi hasashen za a samu matsaikaciyar bunƙasar ta kaso 3.6 a tattalin arziƙin Najeriya a tsakanin shekarun 2025 da 2026 sakamakon sauye-sauyen da gwamnatin tarayyar ƙasar ke gudanarwa.

Bankin ya bayyana hakan ne a cikin rahotonsa, na hasashen tattalin arzikin duniya na bana, da aka wallafa a jiya Alhamis.

Rahoton ya kara da cewa sauye-sauyen baya-bayan nan da gwamnatin Najeriyar ke aiwatarwa sun taimaka wajen bunkasa kwarin gwiwar yin kasuwanci.

KU KUMA KARANTA:Tattalin arzikin Najeriya ya bunƙasa da kaso 3.46 cikin 100 – CBN

Fitattu a cikin sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Najeriyar ke aiwatarwa sune janye tallafin man fetur da kuma kudirorin gyaran dokar harajin da suka janyo cece-kuce.

A cewar bankin duniyar “yawan arzikin da Najeriya ke samarwa, GDP, ya karu da kimanin kaso 3.3 cikin 100 a 2024, inda galibi hada-hadar bangaren ayyuka ne ya samar da shi, musamman bangarorin hada-hadar kudi da harkokin sadarwa.

“Ana hasashen bunkasar arzikin Najeriyar ta kara fadada zuwa kimanin kaso 3.6 cikin 100 tsakanin shekarun 2025 zuwa 2026. Sakamakon manufar takaita hada-hadar kudi ta 2024, ana hasashen raguwar hauhawar farashi sannu a hankali, inda za ta tallafawa bunkasar bangaren ayyuka, wanda ya kasance babban jigo na samun bunkasar arzikin.”

Leave a Reply