Bankin Duniya na gargaɗi kan ‘matsananciyar yunwa’ a Gaza

0
118

Bankin Duniya ya bayyana cewa sama da rabin al’ummar Falasɗinawan Gaza na dab da faɗawa cikin halin matsananciyar yunwa.

Ƙungiyar ta ƙasa da ƙasa ta ce daga cikin waɗanda za su iya faɗawa cikin wannan halin har da yara da tsofaffi.

Ƙungiyar ta yi ƙira da a yi gaggawar ceto rayukan Falasdinawa ta hanyar kai magunguna da abinci da sauran ababen more rayuwa a cikin gaggawa.

KU KUMA KARANTA: Falasɗinawa sun yi jana’izar mutum 28 da Isra’ila ta kashe a sansanonin ƴan gudun hijira

A watan Disambar bara bankin ya amince da dala miliyan 35 ga ƙungiyoyin agaji na UNICEF da WFP da WHO domin ayyuka a Gaza.

Waɗannan kuɗaɗen sun haɗa da dala miliyan 10 ga WFP domin ta sayi kayan abinci da kuma tukuicin kuɗi a hannu wanda za a bai wa kimanin mutum 377,000.

Leave a Reply