Ban ce na fi ƴan Najeriya shan wahalar tsadar rayuwa ba — Ɗangote

Attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirka, Alhaji Aliko Ɗangote ya nesanta kansa da wani labari da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta na zamani cewa ya ce ya fi ƴan Najeriya shan wahalar tsadar rayuwa.

Ɗangote ya ce “wasu ne suka ɗauki nauyin yaɗa labarin domin ɓata mini suna, a daidai lokacin da ƴan Najeriya ke cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi saboda wahalhalun da ake fama da su,” kamar yadda sanarwar da kamfaninsa ya fitar ta bayyana.

Shugaban rukunin kamfanonin na Ɗangote ya nemi ƴan ƙasar su yi watsi da labarin, inda ya yi fatan kawo ƙarshen matsalar da ake ciki a Najeriya.

“Duk abin da ya shafi ƴan Nijeriya ya shafe mu”, in ji sanarwar.

KU KUMA KARANTA: Matatar fetur ɗin Ɗangote ta fara samar da dizel da man jirgin sama

Matsalar hauhawar farashi da tsadar rayuwa da matsi na ci gaba da ta’azzara a Najeriya, inda ko a makon da ya wuce wasu al’umma suka yi zanga-zanga a jihar Neja da nufin jawo hankalin gwamnati kan lamarin.

Sai dai gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi suna ta lallashin ƴan ƙasar tare da alƙawarin cewa abubuwa za su yi sauƙi nan ba da jimawa ba.

A sanarwar kamfanin nasa, Ɗangote ya ƙara da cewa, ”an kawo maganar faɗuwar darajar naira da sayen kaya da Dala ne domin cim ma wasu buƙatu na ƙashin kai buƙatun da ba a samu damar biya ba a baya.”

“Mu ma muna sayen muhimman kayan abinci a kasuwa kamar yadda kowa ke saya don amfanin kanmu da kuma bayarwa wajen ciyar da al’umma,” in ji Ɗangote.

Shugaban kamfanin ya kuma bayyana mamaki kan yadda ake neman haddasa saɓani tsakanin Kamfanin Dangote da gwamnatin tarayya, inda ya ce shi ɗan kasuwa ne ba ɗan siyasa ba, don haka babu inda ya yi maganar ƙalubalantar gwamnati.

“Kamfaninmu ya kasance mai bin dokokin ƙasa a ko da yaushe, tare da neman sauƙi ga al’umma da fatan alheri.”

Sanarwar ta nemi ƴan Najeriya su guji ɗaukar saƙon da ba daga kamfanin ya fito ba kai-tsaye, tare da guje wa yaɗa jita-jita.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *