No menu items!

Sample Page Title

Date:

An kama wani bakanike mai shekara 25 yana ƙoƙarin sayar da motar wani mutum da ya ba shi gyara.

Kakakin ’yan sandan Jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya ce bayan karɓar motar daga hannun mai ita don gyara, sai bakaniken ya nufi kasuwa zai sayar.

A cewar Hundeyin, bayan samun sahihan bayanai an kama bakaniken da wata mota ƙirar Toyota Camry mara lamba.

Hundeyin ya ƙara da cewa wanda ake zargin zai fuskanci shari’a da zarar an kammala bincike a kansa.

Ya shawarci masu motoci da su yi taka-tsan-tsan wajen bayar da motocinsu ga amintattun bakanikai.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...