Bai kamata a dinga bai wa ɓarayi muƙamin Ministoci ba – Sarki Sanusi

0
243
Bai kamata a dinga bai wa ɓarayi muƙamin Ministoci ba - Sarki Sanusi
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II

Bai kamata a dinga bai wa ɓarayi muƙamin Ministoci ba – Sarki Sanusi

Daga Jameel Lawan Yakasai

Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana damuwarsa kan lalacewar ɗabi’u a cikin al’ummar Najeriya, yana mai cewa bai dace a ci gaba da ba wa barayin dukiyar ƙasa mukaman gwamnati ba.

A wata hira da aka yi da shi Sanusi ya ce Najeriya na bukatar farfaɗo da ɗabi’u na Daraja da gaskiya, yana mai cewa yawancin shugabannin da suka rike madafun iko sun fi mayar da hankali kan tara dukiya maimakon yi wa ƙasa hidima.

KU KUMA KARANTA: Bai dace rundunar ‘yansanda ta gayyaci Sarki Sanusi ba – Shugaban Bankin Stanbic IBTC

Ya ce rashin tarbiyya da sanin ya kamata shi ne ke haddasa yadda mutane ke shiga gwamnati da niyyar samun kuɗi, inda ya jaddada cewa hakan na ci gaba da lalata ƙasa.

Sanusi ya koka kan yadda mutane da aka sani da sata ke samun karin mukamai, yana mai cewa wannan dabi’a ce da za ta ci gaba da haifar da shugabanni marasa ƙima.

Sarkin ya ce babu yadda shugaban kasa ko ministoci kaɗai za su iya gyara Najeriya, sai kowa ya taka rawarsa. Ya kuma jaddada buƙatar ƙarfafa ma’aikatan gwamnati domin su iya ƙin bin umarnin ‘yan siyasa da ke neman karya doka.

Leave a Reply