No menu items!

Sample Page Title

Date:

Babu wata rashin jituwa ko ɓaraka tsakanina da Kwankwaso – Gwamna Abba

Gwamna Abba Yusuf ya bayyana iƙirari da mara tushe, inda ya jaddada dadewa da kuma karfin dangantakarsa da Kwankwaso.

Gwamnan Kano, Abba Yusuf ya musanta ikirarin samun rashin jitiwa da uban gidansa na siyasa, Sanata Rabiu Kwankwaso, inda yace har yanzu alakarsu mai karfi ce kuma ta ginu ne a kan mutunta juna.

A yayin wata ganawa da manema labarai a Alhamis da ta gabata, Gwamna Yusuf ya yi karin haske game da rade-radin da ake yadawa a tafiyar kwankwasiya dama jam’iyyar NNPP, dake nuna cewa Kwankwaso na yin katsalandan a harkokin gwamnatinsa, inda yake zama tankar “wa’adin mulki na 3 yake yi a boye”.

Gwamna Abba Yusuf ya bayyana kirarin da mara tushe, inda ya jaddada dadewa da kuma karfin dangantakarsa da Kwankwaso.

KU KUMA KARANTA:Gwamna Abba ya ɗauki nauyin kula da marayu 95

“Babu kamshin gaskiya game da rade-radin rashin jituwa a tsakaninmu.” a cewar Abba Yusuf. “yau shakarata 40 da saninsa, ku gaya mini, wane dan siyasa ne zai shafe tsawon wannan lokaci ba tare da sun bata ba?”

Ana zargin cewar dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Dala, Aliyu Sani Madakin-Gini, wanda kwanan nan ya raba gari da kwankwason da kitsa jita-jitar.

Madakin-Gini yayi zargin cewar batutuwan da suka shafi kwangilar sayen magunguna data bada gurbin karatu ne suka haddasa tsamin dangantakar. saidai, Abba Yusuf, ya yi watsi da zarge-zargen, inda ya jaddada ikonsa sannan ya yabawa gudunmowar kwankwaso a rayuwarsa ta siyasa.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...