Babu barazanar da za ta hana mu gudanar da zanga-zanga – Ƙungiyar Matasan Arewa

0
162
Babu barazanar da za ta hana mu gudanar da zanga-zanga - Ƙungiyar Matasan Arewa

Babu barazanar da za ta hana mu gudanar da zanga-zanga – Ƙungiyar Matasan Arewa

Daga Ibraheem El-Tafseer

‘Arewa Youth Ambassadors’ (AYA) Ƙungiyar Jakadun Matasan Arewa, sun ce babu wata barazana da za ta iya hana su gudanar da zanga-zangar da suka shirya yi saboda halin ƙuncin da ake ciki.

Ko’odinetan ƙungiyar ta AYA na ƙasa, Kwamared Yahaya Abdullahi, a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Litinin a Abuja, ya ce rashin samar da ingantaccen tsarin tattalin arziƙi a cikin al’umma barazana ce ga adalci.

Abdullahi ya ce: “Matsalar taɓarɓarewar tattalin arziƙi da kuma matsalolin da muke fuskanta a ƙasar nan, sun samo asali ne daga munanan tsare-tsare da rashin mutuntaka da gwamnatin shugaba Tinubu ta ɗora mana.

Abdullahi ya ce cire tallafin man fetur da aka yi ba zato ba tsammani ya jefa al’umma cikin halin ƙunci. Ya ƙara da cewa, “rashin abinci da ba da kuɗi a abokai da ‘yan uwan ​​wadanda ke da madafan iko abu ne da ba za a amince da shi ba, kuma ba zai magance mana matsalolinmu ba. A dawo mana da tallafin mai kawai yanzu.”

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda sun sha alwashin daƙile tashe-tashen hankula a lokacin zanga-zanga

Ya ce an sha wahalar da ‘yan Najeriya ta hanyar kalaman riƙon sakainar kashi da kuma manufofin tattalin arziƙi na ƙarya.

Wannan a cewarsa ba su da wani zaɓi da ya wuce bayyana ɓacin ransu ta hanyar da ta dace.

“Muna zanga-zangar haƙƙinmu ne, dole ne mu yi zanga-zangar adawa da rashin shugabanci nagari. Ba za mu iya ci gaba da zama a matsayin bayi a ƙasarmu ba, dole ne mu yi magana kuma mu yi yaƙi don kanmu, babu wanda zai iya yi mana.

“Dole ne matasa su fito kan titi a ranar 1 ga watan Agusta kuma da zarar gwamnati ta gaza kawo ƙarshen waɗannan bala’o’in da suka jefa mu cikin talauci da yunwa, za a ci gaba da zanga-zangar har zuwa ranar 10 ga Agusta, 2024 ko ma zanga-zangar ta ci gaba.

“Dole ne mu yi aiki don kawo sauyi a ƙasar ubanmu, gwamnati ta gaza kuma dole ne matasa su yi aiki, mutane suna mutuwa cikin yunwa kuma babu wanda ya damu. Babu wata al’umma da za ta iya rayuwa da yunwa, ko da ruwa.

“Saboda haka zanga-zangar da muka shirya ta zama dole kuma babu makawa, babu ja da baya. Abin da zai dakatar da zanga-zangar nan kawai shi ne, mu ga gwamnati ta canza akasin haka don ‘yan Najeriya su samu nutsuwa,” Abdullahi ya ƙara da cewa.

Leave a Reply