Babu ƙaramar hukuma ko ɗaya a hanun Boko Haram – Gwamna Zulum

0
218

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, a ranar Juma’a, ya ce al’amuran tsaron jiharsa sun inganta da kaso 85% cikin 100, yana mai cewa babu wani yanki da ke ƙarƙashin ikon Boko Haram.

Zulum ya bayyana hakan ne bayan ya fito daga ganawar sirri da ya yi da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, a fadar Aso Rock da ke Abuja, cewar rahoton The Punch.

“Magana ta gaskiya, babu ɗaya daga cikin ƙananan hukumomi 27 na jihar Borno da ke ƙarƙashin ikon ‘yan tada ƙayar baya.” A cewarsa.

A cikin shekaru 14 da suka gabata jihar Borno da jihohin Arewa maso Gabas na Adamawa da Yobe sun zama matattarar ayyukan ta’addanci na Boko Haram.

A cikin watan Yunin 2021, hukumar ci gaban majalisar ɗinkin duniya ta ƙiyasta aƙalla mutuwar mutane 350,000 daga tashe-tashen hankula da Boko Haram tun shekarar 2009.

Da aka tambaye shi halin da ake ciki, Zulum ya kaɗa baki ya ce: “Gaskiya lamarin tsaro ya inganta a jihar Borno da sama da kaso 85% cikin 100. Ayyukan tattalin arziƙi na ci gaba da tafiya daidai a jihar Borno.”

KU KUMA KARANTA: Zulum ya raba wa iyalai dubu 40 tallafin abinci da kuɗi a Konduga

“Na karanta wani rubutu a kwanakin baya na cewa ana samun ƙaruwar ta’addanci a jihar Borno, labarin ba gaskiya ba ne. Sojojin Najeriya suna ba mu haɗin kan da ake so, ‘yan sanda, rundunar sojin sama da sauran sassan rundunar sojin Najeriya suna tallafa mana.”

Sai dai, Gwamnan ya ce wasu ƙananan hukumomin da har yanzu ake fama da rikici na tsawon shekaru da dama, mutane ba su gama komawa gaba ɗaya ba.

“Yanzu, an sake tsugunar da mutane a wani ɓangare, musamman a ƙaramar hukumar Abadam sai kuma ƙaramar hukumar Guzamala.” A cewarsa.

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya raba tallafi ga sojojin da suka samu raunika a wajen yaƙi da ‘yan ta’addan Boko Haram.

Gwamna Zulum ya raba Naira miliyan 10 ga sojojin domin rage raɗaɗin raunikan da suka samu yayin fafatawa da ‘yan ta’adda.

Leave a Reply