Babban hafsan tsaron ƙasa ya zargi wasu ƙasashe da rashin adalci na ƙin sayar wa Najeriya makamai

Babban hafsan tsaron Najeriya ya bayyana takaicinsa a ranar Talata kan abin da ya ƙira rashin adalcin wasu ƙasashen da ke ƙin sayar da makaman soji wa Najeriya ta wajen rabewa da buƙatar kare haƙƙin bil’adama.

Kalaman na Janar Christopher Musa na ƙara jaddada ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da ƙasar da ta fi yawan al’umma a nahiyar Afirka ke fuskanta wajen yaƙi da matsalar tsaro mai cike da sarƙaƙiya.

“Duk da kuɗinmu, yana da wuya mu samu kayan aiki,” a cewar Musa ga manema labarai a Abuja babban birnin Najeriya, inda ya tabbatar cewa akwai matuƙar buƙatar kayayyaki kamar su jirage masu sauƙar ungulu, jirage marasa matuƙa da kuma motoci masu sulke.

Jami’an tsaron Najeriya sun kwashe shekaru da dama suna fuskantar zarge-zargen kashe-kashen ba bisa ƙa’ida ba da kuma kame ba bisa ƙa’ida ba. Akwai lokacin da Amurka da sauran manyan masu samar da makamai suka hana sayar da makamai saboda zarge-zargen.

A cikin watan Disamba, aƙalla fararen hula 85 ne suka mutu a lokacin da wani jirgin sojin Najeriya mara matuƙin ya kai hari kan jama’a lokacin wani taron addini a Kaduna na yankin arewa maso yammacin Najeriya, wanda shi ne na baya bayan nan cikin jerin irin waɗannan lamuran.

KU KUMA KARANTA:Kotunan da mu ke da su a Najeriya sun wadata wajen shari’un cin-hanci – Shugaban ICPC

Musa ya ce rundunar sojojin Najeriya na ci gaba da inganta ayyukanta na kare haƙƙin ɗan adam kuma ta na hukunta jami’anta masu laifi. A yanzu haka ana gudanar da bincike kan zargin cin zarafi, kuma nan ba da jimawa ba za a fitar da rahoto kan harin na watan Disamba, in ji shi.

Sai dai kuma, babu wata shaida da ke nuna cewa sojojin Najeriya sun samu ci gaba a fannin kare haƙƙin bil’adama, a cewar Isa Sanusi, darektan kungiyar Kare Haƙƙin Ɗan Adam ta Amnesty International a Najeriya.

Tallafin da sojojin Amurka ke bai wa Najeriya a wasu lokuta ya kan haɗa da horo kan yadda za a daƙile haɗurran da ke rutsawa da fararen hula, kamar yadda wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar a watan Janairu kan haɗin gwiwar tsaro.

Sanarwar ta ce a cikin watan Agusta ne Najeriya ta bayar da kuɗin farko na jiragen sama masu sauƙar ungulu guda 12 da kuɗinsu ya kai dala miliyan 997.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *