Babban hafsan sojin Isira’ila zai yi murabus
Babban hafsan sojin Isra’ila, Herzi Halevi, ya ce zai yi murabus a ranar 6 ga watan Maris, kuma ya ce ya dauki alhakin gagarumin gazawa ta fuskar tsaro da aka samu a harin ranar 7 ga Oktoba, 2023.
A cikin wata wasika da ya aike wa ministan tsaron Isra’ila, Halevi ya ce zai kammala binciken da sojojin Isra’ila suka yi kan harin na watan Oktoba wanda ya yi sanadin barkewar rikicin da aka shafe watanni 15 ana yi.
KU KUMA KARANTA:Paparoma Francis ya yi Alla-wadai da matakan Sojin Isra’ila a Gaza
Duk da ya yake yarjejeniyar tsagaita bude wutar ta fara aiki na tsawon makonni shida, Halevi ya ce, “ba a cimma manufar yakin ba, sojojin za su ci gaba da fafatawa don kara wargaza kungiyar Hamas da karfin mulkinta, da tabbatar da dawowar wadanda aka yi garkuwa da su. ‘Yan Isra’ila da suka rasa muhallansu sakamakon hare-haren ‘yan bindiga kuma sun koma gida.”
Hamas ta ce za ta sake sakin wasu mutanen da ta yi garkuwa da su a ranar Asabar, yayin da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Isra’ila ta shiga kwana na uku, yayin da hukumomin agajin jinkai na Majalisar Dinkin Duniya su ka kai kayan agaji Gaza domin taimaka wa fararen hula Falasdinawa.