Ba zan taɓa juyawa APC baya ba – Buhari

0
19
Ba zan taɓa juyawa APC baya ba - Buhari

Ba zan taɓa juyawa APC baya ba – Buhari

Tsohon Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya ce jaddada matsayarsa ta ci gaba da zama matsayin mamba a jam’iyyar APC mai mulki.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis ta hannun kakakinsa Malam Garba Shehu, Buhari ya ce shi da APC – mutu ka raba.

“Ni mamba ne a APC kuma ina so a rika kirana a matsayin hakan. Zan yi iya bakin kokarina na ga na tallata APC ta kowacce hanya.” Buhari ya ce cikin sanarwar.

KU KUMA KARANTA:Ana zargin tsoffin shugabannin Najeriya Obasanjo da Buhari da awun gaba da dala biliyan 6 na kwangilar wutar Mambilla

Kalaman na Buhari na zuwa ne sa’o’i bayan da tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El Rufa’i ya ce ya fadawa Buhari cewa zai fita a jam’iyyar ta APC.

A farkon makon nan El Rufa’i ya sauya sheka ya koma jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) mai alamar doki yana mai zargin jam’iyyar da kaucewa manufofin da aka kafata akai.

Sai daia sanarwar ta Garba Shehu, Buhari ya ce, “ba zai taba juyawa jam’iyyar baya ba wacce ta bas hi wa’adin mulki biyu a ofis.”

Leave a Reply