Connect with us

Labarai

Ba zan mayar da wani yanki na Najeriya saniyar ware ba – Tinubu

Published

on

Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Najeriya, Alhaji Bola Ahmed, ya yi alƙawarin yi wa ƙasa ayyukan ci gaba daidai-wa dai da, ba tare da nuna wariya ga wani ɓangare ba.

Tinubu ya bayyana haka ne a wata takardar manema labarai, wanda Ofishin zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ta fitar, wanda Abdulaziz Abdulaziz ya sanya wa hanu.

Asiwaju Tinubu, wanda za a rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa a ranar 29 ga wannan wata na Mayu, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas.

Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar yana ziyarar kwanaki biyu ne a jihar domin ƙaddamar da ayyukan da gwamnatin Nyesom Wike ta aiwatar.

“Ba zan mayar da wani yanki saniyar ware ba, amma zan bar ayyukan da ba za a manta da su ba a faɗin Nijeriya,” in ji shi a yayin buɗe gadar Rumuokwuta/Rumuola.

Tinubu ya yabawa Gwamna Wike bisa ayyukan ci gaba da ya cimma a jihar Ribas, musamman gadar sama 12 da aka gina a faɗin babban birnin jihar, inda ya ce lallai tarihi zai riƙa tunawa da shi.

Ya ce da irin nasarorin da ya samu a jihar, Nijeriya za ta buƙaci gwamnan Ribas ɗin mai barin gado a manyan muƙamai.

A ɓangaren siyasa, Tinubu ya godewa Wike da al’ummar jihar Ribas bisa goyon bayan da suka ba shi.

Ya ce yana jihar ne bisa alƙawarin da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe a Ribas, inda ya ce “idan ka yi alƙawari, ka cika shi.

“Ba zan taɓa mantawa da muhimmiyar rawar da manya da kuma al’ummar jihar nan suka taka ba a yaƙin neman zaɓen da na yi na zama shugaban ƙasar nan. Kuna da godiyata ta har abada.

“A mai girma Gwamna Wike, na ga mutum mai ƙa’ida. Ya ɗauki matakin da ya dace na cewa a mayar da shugabancin ƙasarnan Kudu, kuma ya samu ƙwarin guiwar jajircewa kan matsayarsa, ba tare da la’akari da wa hakan zai ɓatawa ba.

“Haƙiƙa shi mutum ne mai mutunci. Bai zaɓi biyan buƙatar kansa ba, a’a, ya zaɓi biyan buƙatar ƙasa da al’ummar jihar Ribas, ina gode masa bisa wannan jagorancin na sadaukar da kai,” inji shi.

A nasa jawabin, Wike ya ce gayyatar da aka yi wa Tinubu domin ƙaddamar da ayyuka a jihar cika alƙawari ne da aka yi a ziyarar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a Ribas.

KU KUMA KARANTA: Shugaban ƙasa mai jiran gado, Tinubu ya dawo gida, ya ce “a shirye nake da aikin da ke gaba”

Ya kuma godewa Tinubu kan yadda ya amince ya ziyarci jihar Ribas tare da ƙaddamar da ayyukan.

Wike, wanda ya caccaki shugabannin jam’iyyarsa ta PDP, ya yaba da zaɓen Tinubu wanda a cewarsa, ya kunyata masu zagon ƙasa.

Taron ya samu halartar Kakakin majalisar wakilai Hon. Femi Gbajabiamila da Gwamna Abubakar Badaru (Jigawa), David Umahi (Ebonyi), Abdulrahman Abdulrazaq (Kwara), Seyi Makinde (Oyo) da Hope Uzodinma (Imo).

Sauran sun haɗa da tsoffin gwamnoni Dr Peter Odili (Ribas), Cif Bisi Akande (Osun), Cif James Ibori (Delta), Dr Kayode Fayemi (Ekiti), Cif Timipre Sylva (Bayelsa) da Cif Ayo Fayose (Ekiti).

Sauran waɗanda suka halarci taron sun haɗa da zaɓaɓɓen gwamnan jihar Ribas, Mista Sim Fubara, Ministan matasa da ci gaban wasanni, Mista Sunday Dare, Mista Dele Alake da kuma Alhaji Kashim Ibrahim Imam, da dai sauransu.

1 Comment

1 Comment

  1. Pingback: Gwamnatin Tinubu, ba za ta musuluntar da Najeriya ba – Shettima | Neptune Prime Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Al'ajabi

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Published

on

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon bene mai hawa biyu a Jihar Legas, ya rushe yayin da ake tsaka da mamakon ruwan sama wanda ya haddasa ambaliya a wasu sassan jihar.

Ginin ya rushe ne a lamba 12 da ke yankin Cameroun kusa da Ewenla a Mushin.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (LASEMA), ta bayyana cewar bayan isar jami’anta wajen da lamarin ya faru, ta gano wani sabon gini mai hawa biyu ya rushe.

An ceto mutum bakwai; mata uku da maza huɗu, tuni aka kai su asibiti domin duba lafiyarsu.

KU KUMA KARANTA: Wani bene mai hawa 4 ya rufta da mutane a Abuja

Ya zuwa yanzu dai hukumar, ta ce babu wanda ya mutu a dalilin rushewar ginin.

Babban sakataren LASEMA, Dokta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya ce ana ci gaba da gudanar aikin ceto don tabbatar da babu wanda ya maƙale a baraguzai.

Continue Reading

Labarai

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Published

on

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewar wani jami’in Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC), ya hallaka kansa har lahira a Abuja.

An tsinci gawar marigayin ne a gidansa da ke babban birnin tarayya.

Marigayin, wanda ba a bayyana sunansa ba, an ce ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka yi kwas na 5 a makarantar horas da masu yi wa ƙasa hidima ta hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa.

An ruwaito cewar yana da ƙwazo da himma a wajen gudanar da ayyukansa.

Wata majiya ta ce jami’in ya jima yana fama da baƙin ciki da matsalolin rayuwa kafin mutuwarsa.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya shaida wa manema labarai cewa hukumar za ta binciki musababbin da ya sanya ya kashe kansa, kuma hukumar za ta taimaka wa iyalansa.

Oyewale, ya ƙara da cewa hukumar za ta binciki wasu abubuwa da suka haɗa da matsalar taɓin hankali da kuma matsalolin iyali waɗanda ka iya sanya ma’aikacin kashe kansa.

KU KUMA KARANTA: Ana zargin wani jami’in kwastam ya kashe kansa a Abuja

Sai dai ya ce hukumar ba za ta fitar da wata sanarwa ko kuma bayyana sunan jami’in ba, har sai an kammala bincike.

Continue Reading

Labarai

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Published

on

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), ta rufe shaguna kusan 100 a babbar kasuwar Ogbete ta Jihar Enugu, bisa zargin sayar da wasu abubuwan sha na jabu.

Daraktan NAFDAC, Martins Iluyomade a yankin Kudu maso Gabas, ya ce hukumar ta ɗauki matakin ne bayan wani samame da ta kai a ranar Litinin.

A yayin samamen jami’an hukumar NAFDAC, sun cafke wata babbar mota ɗauke da kayayyakin maye tare da cafke wasu ‘yan kasuwa huɗu da ake zargi da hannu wajen sayar da jabun abubuwan sha.

Iluyomade, wanda masanin haɗa magunguna ne, ya nanata cewa matakin ya zama dole domin kare masu amfani da ire-iren kayayyakin .

Ya ce waɗanda ake zargin a halin yanzu ana kan bincikensu kuma za su fuskanci tuhuma a gaban kotu bayan kammala binciken.

KU KUMA KARANTA: NAFDAC ta haramta amfani da maganin tari na yara na kamfanin J&J

Har wa yau, ya nanata ƙudurin NAFDAC na kawar da kayayyaki marasa inganci, da jabun abubuwan ci da sha, da gurɓatattun kayayyaki a kasuwa.

Ya ƙara da cewa, an gudanar da binciken ne tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro.

A gefe guda kuma, ya bayyana muhimmancin aikin hukumar na tabbatar da lafiyar al’umma.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like