Ba za mu sayar da matatar mai ta Fatakwal ba – NNPC
Daga Jameel Lawan Yakasai
Kamfanin NNPC ya musanta jita-jitar da ke yawo kan cewa zai sayar da Kamfanin Matatar Mai na Port Harcourt. Shugaban kamfanin, Bayo Ojulari, ya bayyana hakan a wani taron ma’aikata da aka gudanar a Abuja, yana mai jaddada cewa kamfanin zai ci gaba da gyara matatar da kuma riƙe mallakinta.
Ojulari ya ce sayar da matatar ba zai amfanar da ƙasar ba, yana mai cewa matsayar kamfanin ba sabon abu ba ne, sai dai sakamakon binciken fasaha da na kuɗi da ake yi kan matatun Port Harcourt, Kaduna da Warri.
KU KUMA KARANTA: An sauƙe Mele Kyari daga shugabancin NNPC, Bashir Bayo ya maye gurbinsa
NNPC ya bayyana cewa sai an kammala gyara matatar tare da haɗin gwiwar ƙwararrun masu fasaha kafin a fara cikakken aiki, yana mai cewa sayar da ita yanzu zai rage kimar ta.









