Ba za mu iya ci gaba da biyan kuɗin tallafin wutar lantarki ba – Gwamnatin Najeriya

0
193

Daga Ibraheem El-Tafseer

Ministan lantarki na Najeriya, Adebayo Adelabu, ya ce ƙasar ba za ta iya ci gaba da biyan kuɗin tallafin wutar lantarki ba.

Ya ce dole ne ƙasar ta fara ɗaukar matakai don magance basukan da kamfanonin samar da wutar ke bin gwamnati, inda a yanzu ya ce bashin da kamfanonin ke bin gwamnatin ƙasar ya kai naira tiriliyan 1.3, waɗanda su kuma kamfanonin samar da gas ke binsu bashin naira biliyan 1.3.

Mista Adelabu, wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gabatar a Abuja, ya ce kasafin kuɗin wannan shekara ya ware naira biliyan 450 don biyan tallafin, a yayin da ma’aikatar lantarkin ke buƙatar fiye da naira tiriliyan biyu don biyan tallafin.

Ya ƙara da cewa a yanzu za a bai wa gwamnatocin jihohi damar samar da wutar kansu don raba wa jihohin nasu.

Dangane da yawan faɗuwar babban layin wutar lantarkin ƙasar, wanda ya faɗi aƙalla sau shida tun Disamban da ya gabata zuwa yanzu, mista Adelabu ya ce hakan na faruwa ne sakamakon ƙarancin gas a cikin injunan da ke gudanar da layin, wanda hakan ke sanya shi rashin ƙarfin samar da wutar, tare da lalacewar tasoshin wutar lantarkin musamman yankin arewa maso gabashin ƙasar.

KU KUMA KARANTA: Ƙasar Chaina za ta taimakawa Najeriya wajen gina tashar wutar lantarki

Ministan ya kuma ce kamfanin samar da wutar na Najeriya ya jingine fiye ayyukan 100, saboda samun ƙari a kuɗaɗen kwangilolin ayyukan sakamakon tashin farashin dala, don haka ya ce kamfanin ba zai sake bayar da wasu ayyuka ba, har sai an kammala waɗanda aka riga aka bayar.

Mista Adelabu ya kuma ce an ware fiye da naira biliyan 50 a kasafin kuɗin 2024 don gina ƙananan tasoshin samar da wutar lantarki a yankunan karkara.

Leave a Reply