Ba za mu bar Sahel Alliance ta karkatar da hankalinmu ba – Tinubu

0
126

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ƙungiyar Sahel Alliance da wasu ƙasashen Yammacin Afirka suka yi ba zai karkatar da hankalin ECOWAS daga ayyukan da take yi ba.

Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne a yayin taron ƙungiyar Shugabannin ECOWAS karo na 64 wanda aka gudanar a Abuja a ranar Lahadi.

A kwanakin baya ne ƙasashen Mali da Burkina Faso da Nijar waɗanda ke ƙarƙashin mulkin soja suka kafa ƙungiyar ta Sahel Alliance wadda suka ƙira da yarjejeniyar Liptako-Gourma.

“Da alama wannan haɗakar an yi ta ne da niyyar karkatar da hankalinmu daga abin da muka yarda da shi da ayyukan da muke yi na tabbatar da dimokuraɗiyya da kyakkyawan shugabanci wanda zai iya tasiri a rayukan jama’a.

“Ba za mu bari a karkatar da hankalinmu ba daga cika burin da muka ƙudirin aniyar cimma da kuma bin kyakkyawar turba ta haɗa kan ƙasashen ECOWAS kamar yadda aka tsara a ƙundin tsarin ƙungiyar,” in ji Shugaban na ECOWAS Bola Ahmed Tinubu.

KU KUMA KARANTA: ECOWAS ta gindaya sharuɗa na cire wa Nijar takunkumai

Shugaba Tinubu ya ƙara jaddada cewa duk da irin ƙalubalen da yankin na Yammacin Afirka ke fuskanta, ECOWAS ta samu babbar nasara ta ɓangaren ci gaban yankin.

Ƙungiyar ta ECOWAS tana fuskantar matsaloli da dama a wannan lokaci, daga ciki har da batun juyin mulki da tsaro da matsin tattalin arziki.

An fuskanci juyin mulkin soji tun daga shekarun 2020, kama daga Mali zuwa Burkina Faso da Guinea da Nijar.

A watan da ya gabata, wani yunkurin juyin mulki a Saliyo ya yi sanadin mutuwar mutum 21, kamar yadda manyan jami’an gwamnatin ƙasar suka tabbatar wadda ke cikin ƙasashen ECOWAS.

Ita ma Guinea-Bissau wadda ƙasa ce ta ECOWAS, shugabanta Umaro Sissoco Embalo a ranar Asabar ya ce rikicin da aka yi a wannan makon wanda a ciki akwai wasu daga cikin dogaran ƙasar “yunkuri ne na juyin mulki.”

Leave a Reply