No menu items!

Sample Page Title

Date:

Shugaban ƙasar Senegal Macky Sall ya ce wa’adin mulkinsa zai ƙare ranar 2 ga watan Afrilu kamar yadda dokoki suka tanada, amma bai bayyana ranar gudanar da zaɓen shugaban ƙasar da ya ɗage a farkon wannan wata ba.

Sall ya fuskanci gagarumar suka daga ciki da wajen ƙasar tare da jerin zanga-zanga bayan da haka kwatsam ya ɗage zaɓen shugaban ƙasar da ya kamata a gudanar ranar 25 ga watan Fabrairu zuwa watan Disamba.

Sukar da yake sha da kuma hukuncin da Kotun Tsarin Mulkin ƙasar ta yanke cewa ɗage zaɓen ya saɓa wa doka ne ya sa ya gabatar da jawabi ga ƴan ƙasar ranar Alhamis.

A jawabin nasa, Shugaba Salla ya ce ba zai sanya sabuwar ranar gudanar da zaɓe ba sai an kammala wani taron sulhu na siyasa da za a soma a ƙasar ranar Litinin mai zuwa.

KU KUMA KARANTA: Za mu gudanar da zaɓen Senegal nan ba da jimawa ba – Macky Sall

“Wa’adin mulkina a matsayin shugaban ƙasar Senegal zai ƙare ranar 2 ga watan Afrilu, 2024,” in ji Shugaba Sall, bayan da ƴan ƙasar suka riƙa raɗe-raɗin cewa yana so ya tsawaita wa’adin mulkinsa.

Ya ƙara da cewa: “Amma game da ranar gudanar da zaɓen, za mu ga yadda za ta kaya a yayin da za a yi taron sulhu. Za a iya gudanar da zaɓen kafin ko bayan ranar 2 ga watan Afrilu.”

A wani mataki da ake gani a matsayin yunƙurin rarrashin ƴan ƙasar, Shugaba Sall ya ce yana duba yiwuwar sakin manyan ƴan adawa biyu Ousmane Sonko da Bassirou Diomaye Faye.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...