‘Ba ‘yansanda ba ne suka kuɓutar da ‘ya’yanmu, biyan kuɗin fansa muka yi’ – Iyayen Nabeeha

0
147

Daga Ibraheem El-Tafseer

Idan ba a manta ba, a ƙarshen makon da ya gabata ne, aka sako ‘yanmatan nan biyar waɗanda masu garkuwa da mutane suka sace a Abuja.

Masu garkuwa da mutane sun sace ‘yanmatan guda shida da mahaifinsu ne a gidansu da ke Abuja.

Daga baya suka saki mahaifin yaran mai suna Mansour Al-Kadriyah tare da umartarsa da ya je ya nemi naira miliyan 60 kafin a saki yaran.

Sai dai bayan mako ɗaya, mahaifin yaran bai samu damar biyan kuɗin ba, inda masu garkuwan suka kashe ɗaya daga cikin yaransa mai suna Nabeeha, wadda ba ta daɗe da kammala karatun jami’a ba, sun yi hakan ne a matsayin gargaɗi ga iyayen domin su gaggauta nemo kuɗin fansa.

Haka nan ma a wannan lokacin sun ƙara yawan kuɗin fansar da suke nema.

Hakan ya jawo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta, inda mutane da dama suka fara bayar da gudummawar kuɗi ga iyalan domin a ceto ‘yanmatan.

An saki ‘yan matan ne bayan shafe kwana 19 a hannun masu garkuwa da mutane.

A ranar Talata da dare, mai magana da yawun ‘yan sandan Najeriya reshen birnin tarayya, Abuja, Josephine Adeh, ta sanar da cewa jami’an ‘yan sanda sun kuɓutar da ‘yanmatan.

Wata sanarwa da Adeh ta fitar, ta ce ‘yansanda tare da haɗin gwiwar jami’an sojin Najeriya ne suka samu nasarar ceto yaran.

Sai dai, lokacin da BBC ta tuntuɓi iyalan Al-Kadriyah don jin yadda aka saki ‘yanmatan, abun da suka faɗa ya saɓa da na ‘yansanda da kuma sojoji.

Kawun yaran, Sheriff Al-Kadriyah, wanda malami ne a sashen addini da tarihi na Jami’ar Jihar Kwara, ya bayyana cewa su suka kuɓutar da yaransu.

KU KUMA KARANTA: An ƙuɓutar da ‘yan’uwan Nabeeha daga masu garkuwa da mutane

Sheriff ya ce sun biya kuɗin fansa ga masu garkuwa da mutanen kafin a saki ‘yanmatan.

Ya ce bayan biyan kuɗin da kwanaki huɗu ne masu garkuwar suka ƙira su da su zo su karɓi yaran a jihar Neja.

“Ƴan’uwa ne a cikin iyalai suka haɗu domin biyan kuɗin fansar da kuma fitar da iyalin cikin wahalar da suka shiga.”

“Ba zan iya faɗan nawa muka biya masu garkuwa da mutanen ba domin sakin ‘yanmatan saboda dalilai na tsaro, amma sun karɓi maƙudan kudaɗe a hannunmu.”

Ya ce da gaske ne sojoji sun raka waɗanda suka kai kuɗin domin kare su.

“Ba gaskiya ba ne cewa ‘yansanda ne suka ceto ‘yanmatan ba, mun biya kuɗin fansa kafin sakin su.

“Masu garkuwa da mutanen sun ƙira mu a ranar da suka yi niyyar sakin ‘yanmatan, sannan suka ba mu adireshin wajen da za mu haɗu.

“Sojoji sun bi bayan waɗanda suka je karɓar yaran domin ba su kulawa, babu wani jami’in ɗansanda da ya bi mu.

“Ba wai mun ce ‘yansanda ba su yi aiki ba, sai dai dangane da sakin ‘yanmatan, ‘yansanda ba su kuɓutar da su ba, biyan kuɗi muka yi.”

Sheriff Al-Kadriyah ya gode wa dukkan waɗanda suka taimaka musu da tallafin kuɗi domin sakin yaransu, inda ya ce kuɗin ya taimaka musu sosai wajen ceto yaran nasu.

Ya ƙara da cewa bayan shafe kwanaki 19 a hannun masu garkuwa da mutane, akwai buƙatar duba lafiyar yaran.

Ya ce ‘yanmatan suna asibiti a yanzu inda ake ci gaba da kula da su.

Ya kuma ce mahaifin yaran shi ma yana asibiti, inda yake samun kulawa saboda masu garkuwa da mutanen sun jikkata shi kafin su sake shi ya je ya nemi kuɗi.

“Sun lakaɗa wa mahaifin yaran duka saboda sun faɗa masa cewa ya je ya kawo kuɗi lokacin da yake hannunsu, sai dai ya gaya musu cewa ba shi da kuɗi.”

“Wannan ne ya sa suka lakaɗa masa mugun duka, don haka yana buƙatar kulawa ta lafiya kuma yana karɓar magani da murmurewa.”

“Masu garkuwan sun kashe mutum huɗu ranar da suka kashe Nabeeha.”

Sheriff Al-Kadriyah ya kuma bayyana cewa a ranar da masu garkuwa da mutanen suka miƙa gawar Nabeeha, akwai wasu gawawwaki uku na mutanen da aka kashe.

Don haka ya buƙaci gwamnati da ta shawo kan matsalar tsaro, domin ganin an kawo ƙarshen ayyukan masu garkuwa da mutane a kowace rana a Najeriya.

Leave a Reply