Ba sharholiya za mu yi da kuɗin da muka ware wa kanmu ba – ‘Yan Majalisar Najeriya

0
383

Daga Ibraheem El-Tafseer

‘Yan Majalisar wakilan Najeriya sun fara mayar da martani dangane da sukar da ake musu ta warewa kansu Naira biliyan 70 daga cikin Naira biliyan 500 da suka amince wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kashe, wajen ba wa ‘yan ƙasar tallafin rage raɗaɗin janye tallafin man fetur da gwamnatinsa ta yi.

Da dama daga cikin ‘yan Najeriyar na ganin matakin da ‘yan majalisar suka ɗauka ya nuna yadda suka fi fifita buƙatunsu a kan na jama’a, waɗanda dama ke cikin wahala.

Sai dai a cewar wasu daga cikin ‘yan Majalisar irin su Injiniya Sani Bala Tsanyawa daga Kano, saɓanin yadda mutane ke cewar su za a raba wa kuɗin, za a yi amfani da su ne wajen yin gyare-gyare a majalisar, da biyan albashin ma’aikata masu musu hidima, da sauran ɓangarorin majalisar.

KU KUMA KARANTA: Ba a ƙara wa shugaban ƙasa, mataimakinsa, zaɓaɓɓun ‘yan majalisa da alƙalai albashi ba – Gwamnatin tarayya

Yayin wata hira da BBC, ɗan majalisar ya ce: ”An ware wa wasu ɓangarori da dama nasu kuɗaɗen, me ya sa sai majalisa kaɗai za a sanya wa ido?”

Akwai ‘yan majalisa 469 ciki har da ‘yan majalisar dattawa, kowannensu kuma zai ɗauki ma’aikata guda biyar, ka ga kenan sai ka ninka wannan adadi na 469 sau biyar, dukkansu kuma za a ɗauke su aiki ne daidai da matakin gwamnatin tarayya, kuma sai ka biya su alawus, sai ka kula da wajen zamansu a kwana 28 na farko, don haka da wannan kuɗi za a yi amfani wajen yin duk wannan ɗawainiya,” in ji shi.

Ya yi bayanin cewa Naira biliyan 70 ɗin da suka ware wa kansu na cikin wata Naira biliyan 300 da Shugaba Tinubu ya nema ne tun da farko, ba wai cikin biliyan 500 ɗin da aka keɓe domin rage wa talakawan ƙasar raɗaɗin janye tallafin mai ba.

Ƙungyoyin masu fafutuka a Najeriya sun yi Allah-wadai da matakin ‘yan majalisar, da suke kallo a matsayin harambe da fifita kai.

Ƙungiyar SERAP ta lashi takobin ruga wa gaban kotu, domin ƙalubalantar matakin ‘yan majalisar idan har ba su janye ba.

Sai dai a cewar Injiniya Sani Bala Tsanyawa, ware irin waɗannan kuɗaɗe domin tafiyar da harkokin majalisa ba sabon abu ba ne, domin kuwa yana faruwa a kowa ce ƙasa, kamar yadda ya ce.

”Najeriya ba ƙasa ba ce da ake zaune kara zube, duk abin da aka yi an yi shi ne bisa doka, kuma ba wani sabon abu ba ne,” in ji shi.

Leave a Reply