Ba na neman takarar shugabancin APC – Yahaya Bello

0
109

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce yana biyayya ga jagorancin Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC mai mulki ta Najeriya.

Sakon Yahaya Bello na zuwa ne a lokacin da ake ta yaɗa batun cewa yana neman takarar jam’iyyar kuma za a yi babban taro na zaɓen sabon shugaban APC nan ba da jimawa ba.

A sanarwar da ofishin watsa labaran Yahaya Bello ya fitar a ranar Talata da maraice, ya ce “Muna sane da yadda wasu bata-gari ke yunkurin kawo ruɗani a cikin shugabancin jam’iyyar APC. Wannan aiki ne na wasu jiga-jigan ‘yan adawa da wasu masu zagon ƙasa a cikin jam’iyyarmu.”

A makon nan an yi ta yaɗa batun cewa nan ba da jimawa ba APC za ta yi taron zaɓen sabon shugaban jam’iyya, kuma Yahaya Bello za a bai wa shugabancin, inda har ake wallafa fastocinsa da nufin hakan.

Sai dai sanarwar ta ce “A wani ɓangare na zancen da ake watsawa har da yada hotunan yakin neman zaɓe ɗauke da hoton Alhaji Yahaya Bello, CON, tsohon gwamnan jihar Kogi, ana cewa ya fito takarar shugaban jam’iyyar APC na ƙasa. Labarin ƙage ne, ƙarya kuma ya kamata a yi watsi da shi.”

KU KUMA KARANTA: Ɗan takarar Sanatan APC a Yobe ta gabas, ya yiwa al’ummomin Geidam da Yunusari alƙawarin morar romon dimokuraɗiyya 

Yahaya Bello, wanda ya sauka daga muƙamin gwamnan Kogi a makon da ya wuce bayan ƙarewar wa’adinsa, ya ce jam’iyyarsu ta APC ba ta da wani shiri na gudanar da babban taro ko zaɓen sabon shugaba, don haka babu wata fa’ida ta yaɗa fastocin neman ko wane irin shugabanci a jam’iyya.

“Alhaji Yahaya Bello be bai wa kowa izinin yaɗa wata fosta a madadinsa ba domin ya kasance mai biyayya ga jam’iyya mai kishin jagorancin shugaban jam’iyyar na ƙasa, mai girma Dr Abdullahi Ganduje.”

Dama an daɗe ana yaɗa batun cewa shugabancin jam’iyyar APC na shiyyar Arewa ta Tsakiyar Nijeriya ne a wannan karon, amma babu wani tabbacin hakan da aka ji daga wajen jam’iyyar.

A ƙarshe sanarwar ta yi kira ga jama’a da su yi watsi da “ƙaryar da jama’a ke ta yaɗawa da fastoci don haifar da rashin gaskiya.”

Leave a Reply